Wani direban motar daukar fasinja ya gane wani mutum da ya taba yin garkuwa da shi daga cikin fasinjojin da ya dauka a motarsa a tashar Kwannawa da ke Jihar Sokoto. Direban wanda aka yi garkuwa da shi watanni biyu da suka gabata a Karamar Hukumar Kankara da ke Jihar Katsina ya yi saurin gane mutumin kuma ya sanarwa da shugabbanin tashar.
‘Yan sanda sun kama wanda ake zargin kuma tuni aka mai da al’amarin zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Sokoto don fadada bincike. Wannan lamari ya faru a tashar mota ta Kwannawa da ke Karamar Hukumar Dange-Shuni a Jihar Sokoto, bayan da wannan direba ya shaida wanda ya taba yin garkuwa da shi a cikin fasinjojin da ya dauka a cikin motarsa.
Direban wanda aka sakaya sunansa, an yi garkuwa da shi a Kankara da ke Jihar Katsina watanni biyu da suka gabata. Majiyarmu ta ruwaito cewa direban ya shafe kimanin sati uku a tsare a wurin masu garkuwar bayan biyan kudin fansar da ba’a bayyana adadinsu ba.
Wanda ake zargin ya gamu da cikas, lokacin da ya shiga mota zuwa Kano, ba tare da sanin ita ce motar da suka tare suka yi garkuwa da direba ba. “Direban ya yi saurin gane shi saboda abin bai dade da faruwa ba. “Bayan gane shi, ya yi gaggawar sanar da Shugabannin kungiya su kuma suka sanar da ‘yan sanda mafi kusa,” wani dan kungiyar direbobi NURTW ya shaidawa manema labarai. Shugabannin kungiyar sun canja direban motar da wani bayan motar ta cika da fasinja kuma ya nufi garin Shuni. An ruwaito cewa a nan ‘yan sanda suka kama wanda ake zargin zuwa ofishinsu.
An mayar da wanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Sokoto don fadada bincike. Mai magana da yawun rundunar, DSP Muhammad Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce bincike su ke har yanzu.