Direbobi Na Son Gwamnati Ta Takawa Jami’an Hanyoyin Taraba, Adamawa, Benue Burki

An yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin soja da ’yan sanda da ke jihohin Taraba da Adamawa da Benue da su dauki matakin da ya dace, don hana jami’an su kassara sana’ar tukin manyan motoci a wannan yanki ta hanyar yin kwacen kudi ko tilasta bayar da kudi Naira dubu 1,000 ko 2,000 a shingayen duba ababen hawa da ke wadannan jihohi, al’amarin da ke haifarwa kowane direban babbar mota idan ya yi lodi daga Biu zuwa Port Harcourt sai ya kashe Naira dubu dari daya zuwa dubu 150 kafin ya fita daga Jihohin.
Shugaban kungiyar direbobin manyan motoci reshen tashar Bauchin da ke garin Gombe Alhaji Adamu Juma ya bayyana haka a lokacin da ya kira taron manema labarai a Bauchi, inda ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a iya samun matsala tsakanin su da jami’an tsaron ta hanyar yi musu tirjiya matukar gwamnati ba ta dauki mataki kan wannan kwace da jami’an tsaron ke yi wa direbobin manyan motocin ba. Inda ya bayyana cewa matukar suka yi shiru wannan sana’a da suke yi za ta samu nakasu saboda a halin yanzu iyayen gidanjen su masu motoci da dama sun ajiye wannan aikin wasu sun sa an ajiye motocin saboda babu riba wasu kuma sun samu matsala da direbobin yadda suke ganin kamar ba sa kawo musu kudi amma daga bisani suka fahimci halin da ake ciki suka ajiye motocin su da nufin har sai gwamnati ta gyara lamurran.
Alhaji Adamu Juma ya bayyana cewa suna tare da matsaloli masu yawa a yanayin aiki irin nasu na safara suna shan wahala sosai game da jami’an tsaro da ‘yan iskan kan hanya. Akwai shingen duba abin hawa masu yawa da basa iya lissafa su daga Adamawa zuwa Taraba da Binuwai ya bayyana cewa kowane shingen duba abin hawa kowace mota tana bayar da Naira dubu daya idan kayan abinci ne idan kuma dabbobi ne za a biya naira dubu biyu na tilas saboda sun san mutum ba shi da galihu kuma ba shi da yadda zai kai kukan sa musamman a Jihar Benue abin ya fi muni.
Game kuma da lambobin waya da ake rubutawa a shingayen duba abin hawa na kar mutum ya bayar da cin hanci ya bayyana cewa wannan rubutu duk shirme ne saboda idan ka kira lambobin duk basa shiga. Don haka ya bayyana cewa a halin yanzu suna wahala ne ga jami’an tsaro da man gas saboda idan mutum bai bayar da irin wannan kudi ba dukan tsiya jami’an tsaro za su yi masa ko su masa sharrin da zai gwammace bai shiga wannan sana’a ba. Don haka ya bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta shigowa cikin lamarin saboda an kusa kais u bango, idan sun yunkura sun ce ba za su bayar ba kuma za a iya samun matsala su harbe musu direbobi daga nan kuma ba a san yadda fitinar za ta iya kai wa ba, don haka ya kamata a shigo cikin lamarin tun bai kai ga rasa rayuka da dukiya ba.
Adamu Juma ya kara da cewa a yanzu mutane da dama suna janye jikinsu daga sana’ar sufuri saboda ganin babu riba, musamman a Jihar Taraba, idan mutum ya yi lodi madadin ya bi zuwa Benue ya gwammace ya shiga Gombe da Bauchi zuwa Jihar Filato ya nemi hanyar Port Harcourt saboda uzurawar jami’an tsaron kan hanyar domin zai iya shan mai ya yi zagayen ya kuma samu rarar kudi, domin wadannan jihohi basu da kudin ka’ida irin na wadancan hanyoyi masu yi tamkar fashi da makami. Ya kara da cewa musamman jami’an soja suna yin abin kamar fashi da makami ne saboda abin da suka yanka dole a basu ko su wahalar da mutum su masa sharri, amma ‘yan sanda suna sara suna duba bakin gatari cikin tasu aika aikar ana ciniki suna yin ragi.
Shi ma Malam Hamisu Sale wani direba daga Jihar Gombe ya bayyana cewa daga Adamawa zuwa Taraba da Benue uzurawar jami’an tsaro a kullum tana karuwa ne ba sassauci, saboda ko cikin makon da ya wuce ya tashi daga Biu ya yi lodi ya rike naira dubu dari a hannun sa amma zuwa Zaki Biyam kudin ya kare sai da ya nemi wasu kudin kafin ya ci gaba da bayar wa a kan hanya ya kammala tafiyar a kan naira dubu dari da hamsin. A halin yanzu abin ya zamo tamfal fashi da makami jami’an tsaro ke yi inda suke sa yara ‘yan iska suna sanya manyan itatuwa a kan hanya a gefe ga jami’an tsaro su yara ‘yan iskan ke amsar kudi da yamma kuma soja su zo su karbi nasu a wajen su ‘yan sanda suma su zo su amshi nasu Cibil Defemce suma su zo su karbi nasu. Idan sun koka wa jami’an tsaron da ke kusa da yaran sai su ce mutum ya biya kurum ya wuce ba abin da za su yi wa yaran ashe ‘yan koron su ne.
Hamisu Sale ya bayyana cewa soja sun fi ‘yan sanda basu matsala tamkar barayi suke, idan mutum ya zo Gboko shiga da fita kowane gate Naira dubu haka Zaki Biyam haka wukari da duk wani wajen jami’an tsaro da ke kan hanyar. Matukar mutum bai bayar da wannan kudi ba soja zai iya cewa ya yi birgima a kasa ko ya shiga ruwa ya kwanta da sauran wulakanci. Amma su ‘yan sanda suna taka tsantsan game da duk wani abin da suke yi a kan hanya saboda suna tunanin idan lamarin ya baci suna rasa aikin su amma soja basa wannan tunanin, suna karbar kudin da suka yanke wa direba ba ragin ko kobo ko su yi wa mutum sharri ko su azabtar da shi saboda ya hana su kudi lamarin da suke yi kamar fashi da makami don arzuta kan su.
Don haka Malam Hamisu Saleh ya bayyana cewa nan bad a jimawa akwai yiwuwar su dakatar da gudanar da aiki har sai yadda hali ya kasance matukar ba a dauki matakin da ya dace ba don gujewa shiga tashin hankali su da dukiyar su don a samu bin doka da oda da ingancin zaman lafiya, saboda duk wani mataki da ya dace su dauka sun bi amma lamarin ya faskara.

Exit mobile version