Wadansu direbobin motocin bas-bas masu jigilar fasinjoji daga a Arewacin Nijeriya zuwa Legas a karkashin jagorancin shugaban kungiyarsu na unguwar Sabo Ikorodu dake cikin garin Legas, Malam Ibirahim Abdullahi, sun koka a game da kalubalen da suke fuskanta a kan hanyarsu ta tasowa daga Arewacin Nijeriya shigowa Legas da sauran garuruwan da suke sauke al’umma baki daya.
Direbobin wadanda suka gudanar da wadannan korafe-korafen nasu a unguwar Sabo Ikorodu a lokacin da suke bayyana wa Malam lbrahim, shugaban kungiyar tasu na sabo Ikorodu, irin wadannan matsaloli da suke fuskanta a hanyoyin nasu baki.
Bala Idiris dan asalin unguwar Wanzamai ta karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, yana daya daga cikin direbobin da suka gudanar da irin wannan korafi inda ya cigaba da cewa babu shakka suna fuskantar munanan matsaloli a kan hanyar su ta shiga cikin garin Legas a wajen dogarawan hanya a yayin da suke tsayar da su domin duba takardun motarsa ko lasisinshin tuki ya ce ba za su tambayi komai ba sai su ce ka basu na goro idan ka basu na goron sai su ki karba su ce wai ya yi kadan karshenta su yanko kudi masu yawa kuma sai ka basu san nan kà wuce.
Ya kara da cewa kuma gaba dayan bangarorin dogarawan hanyar haka suke yi masu a cewarsa da fatan gwamnati za ta sanya baki a bisa kan wannan al’amari. Shi ma da yake tabbatar da faruwar wannan al’amari wani daga cikin direbobin Haruna Usman yaron aiki dan asalin karamar Hukumar funtuwa inda shi ma ya cigaba da cewa babu shakka wadannan ma’aikata na kan hanya zuwa Legas suna takura wa direbobi a kan hanya domin kuwa Idan za kaje Legas da motar kaya ko ta fasinja bayan ka ware kudin mai sai kasake ware kudin dogarawan hanya Idan ba haka ba komai yana iya faruwa a kanka ko kuma motarka.
Ya ce a kan haka yake shawartar gwamnati da ta sanya bakin ta a tsakanin direbobin motoci masu bin hanya zuwa Legas da ma’aikatan kan hanyar a wajen shawo kan matsalolin dake tsakanin direbobi da jami’an tsaron da suke kan hanyar zuwa Legas. Suleman zare idonka, shi ma dan asalin karamar Hukumar Malumfashi dake cikin Jihar Katsina, na daga cikin direbobi masu bin wannan hanya ta zuwa Legas ya ce da cewa lallai gaskiya ne jami’an tsaro suna yi wa direbobi yanda suka ga dama a hanyarsu ta zuwa Legas, a domin kuwa sai ka zama janwuya sannan kudi kalilan su shigar da kai cikin Legas a mIsalin kudin da zaka kasha ma jami’an tsaro dake bisa hanyar in ji shi.
musamman bIO da Road safety, da fatan za su gyara aikin su su rika gudanar da shi a cikin adalci iliyasu Abdulbasiru Yalo na unguwar Tudu dake karamar Hukumar kankara da shugaban kasuwar tasu ta direbobin sabo Ikorodu Malam lbirahim Abdullahi da sauran direbobin da suka yi tsokaci a bisa wadannan matsaloli duk kan jawaban su ya karkata ne a wajen gwamnati ta sanya bakinta a wajan matsalolin dake tsakanin direbobi da jami’an tsaro dake bisa kan hanyar zuwa Legas.