Diyar Obasanjo Ta Dirar Ta Karyata Zargin Ragargazar Babanta

Sanata Iyabo Obasanjo ita ce ‘ya ta farko ta tsohon shugaban kasa Oludegun Obasanjo, ta nuna  rashin jin dadinta, akan maganganun da ‘yan barandar, mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta yadda suke dawowa da wabi abin da aka manta da shi. Shi al’amarin ya shafi mahaifin ta ne maganar da ya yi wadda shawara ce da kuma gaskiyar al’amari, amma su suna kare wannan mulki wanda ake ciki.

A wata takarda mai zafi wadda ta aika ma jardar Banguard daga jihar Birginia Amurka, Sanata Obasanjo ta soki mulkin Muhammadu Buhari saboda yadda yake kaucema al’amuran da suka kamata, ayi abin da ya sa shi mahaifin nata har ya kai ga bara. Saboda ai gaskiya ce ya  fada, tana nufin wasikar da ya fitar ranar Talata.

Ta ce, ‘maimakon a yi amfani da wasu shawarwari da ya bada, sai ta nuna jin dadinta akan yadda, wasu ‘yan bami na iya masu goyon Buhari, da su maimakon su yi magana akan wasu muhimman al’amuran da ya yi, amma sai suka kauce suna ta wasu maganganu daban. Ga dabaru a cikin maganar da mahaifin nata ya fada saboda ai ba wani abin da yafi shawara’.

Ta ce ita wasikar ta yi kama da da irin wadda shi tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta ma tsohon shugaban kasa Gooluck Jonathan. Ta kara jaddada cewar ita ba tada ata dangantaka tsakanin mulkin mulkin Muhammadu Buhari , ko kuma Goodluck Jonathan.

Ta kara bayanin cewar, ‘kamata ya yi idan mai hikima ya bada shawara ayi magana da ita, adanda suka buga takarda ta farko, ya dace ace suna  da lokacin da zasu mayar da martini. Sanatar dai ta kasance ne a mukamin Sanata daga sheakarar 2007 zuwa 2011.

Sanata Obasanjo wanda yanzu Farfesa ce a wata jami’ar da take Birginia, a wasikar data aiko  inda ta ce, ‘An tuna mani da wata wasika wadda aka buga 2013, wadda tsohuwar takarda ce, wadda wasu abubuwan da suka faru, sun sa ba tada wani amfani. Ni abin yana bani mamaki maimakon su ga aihairin da yake cikin wasikar, amma sai su ka mayar da ita ta kasance abar tsana da mafani da ita, domin cimma wata  dama tasu’’.

‘’Don an ce Nijeriya nada matsala ai ba barna bane, kuma gaskiya ce domin da akwai matsaloli ma, masu wayo ya kamata su gana haka, wadanda suka karanta wasika ta farko, suka kuma dauki lokaci, su yi ani abu akan duk abubuwan da suka kunsa, wanda abin ne ma yasa suka ba shugaban kasa Buhari da ya yi ko yi da sauran tsofaffin shugabannin kasa, a shekarar 2019. Ni a ganina shawara ce mai kyau, kuma wadda ta dace, idan aka tuna shekarun baya ya yi fama da rashin lafiya.’

Exit mobile version