Diyar Sardaunan Sakkwato Ta Rasu

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,

Diyar Sa Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) Hajiya A’ishatu Ahmad Marafa Dan-Baba ta rasu yau ta na da shekaru 76 bayan fama da rashin lafiya. Ta rasu shekaru 55 bayan rasuwar mahaifinta.

Hajiya Ai’sha wadda aka fi sani da Gwaggo A’i ita ta rasu ne a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa kamar yadda wani makusancin gidan Hassan Muhammad Binanchi ya bayyanawa LEADERSHIP A YAU.

Dattijuwar marigayiyar ita ce matar Marafan Sakkwato, Ahmad Dan-Baba wanda ya rasu a 1982 kuma mahaifiyar Magajin Garin Sakkwato, Hassan Marafa Dan- Baba, Jikan Sardauna kuma dan ta na hudu wanda babban Basarake ne kuma daya daga cikin masu zaben Sarkin Musulmi.

Gwaggo A’i wadda rahotanni suka bayyyana cewar ta fi sauran ‘ya’yan Sardauna kusanci da mahaifinta da aka yi wa kisan gilla a kazamin juyin mulki a 1966, a lokacin ta na da shekaru 20.

Majiyar LEADERSHIP A YAU ta bayyana cewar za a dauko gawarta daga Dubai zuwa Sakkwato domin yi mata jana’iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. A yanzu haka a gidan a na cikin alhini, firgici da juyayin rasuwar Gwaggo wadda aka shaida da mutunci, dattako da taimakon al’umma.” In ji Binanchi.

A yanzu haka Hajiya Luba, matar marigayi Marafan Sakkwato, Umaru Shinkafi ita ce kadai ta rage a cikin ‘ya’yan Gamji Dan Kwarai, dukkanin ‘yan uwanta hudu sun kwanta dama.

Exit mobile version