Abba Ibrahim Wada" />

Djokobvic Ya Sha Da Kyar A Hannun Go Soeda

Nobak Djokobic ya yunkuro a ranar Laraba a gasar kwallon Tennis ta Japan Open, inda ya wargaza babban kalubalensa, Go Soeda da ci 6-3 7-5 ya tsallaka zuwa matakin daf  dana kusa dana karshe.

Dan wasan, wanda shine lamba daya a duniya ya ce yana jin radadi a kafadarsa da ya ji raunin da ya hana shi fafatawa a gasar US Open, yayin da yake shirin karawa da dan wasan Faransa, lamba 5 a duniya Lucas Pouille a filin Ariake Coloseum, inda za a yi gasar Olympic ta Tokyo a 2020.

Djokobic na cikin samun nasara ne sai kwatsam dan kasar Japan din mai shekaru 35 da suke karawa ya kara azama, ya zame wa Djokobic alakakai, har wasan da yake 5-3 ya kasance 5-5, sakamakon kurakuran da lamba dayan ya dinga yi.

‘Na yi mamaki yadda nafara wasan cikin nasara amma daga baya kuma abubuwa suka fara canjawa saboda na yi zaton n agama samun nasara sai daga baya na fahimci ya sake samun karfi sosai” in ji Djokobic

Ya ci gaba da cewa “Amma yanzu komai ya kare tunda na samu nasara mai wahala saboda wannan nasarar tana daya daga cikin nasarorin da bazan tabamantawa dasu ba a wasannin na na Tennis a duniya”

A karshe Djokobic ya godewa miliyoyin magoya bayansa da suka tayashi murna kuma suka kasan ce tare dashi a lokacin da ya yi jinya wadda tasa bai halarci gasar cin kofin US Open ba a watan daya gabata.

Exit mobile version