Connect with us

MANYAN LABARAI

Dogara Bai Halarci Babban Taron Jam’iyyar APC Ba

Published

on

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara bai halarci babban taron gudanarwa na Jam’iyyar APC mai mulki ba, wanda yanzu yake gudana a babban ofishin majalisar dake Abuja.

Shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole ya karanta wasikar neman uzurin rashin zuwa da Dogara da mataimakin shi Yusuf Lasun suka aikawa jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar na kasa Bola Tinubu shi kuwa ya zo taron ne zuwa bazata, saboda a hukumance shi baya cikin kwamitin gudanarwa na Jam’iyyar.

An fara taron ne karfe 11:20 daidai na safe, daga isowar shugaban kasa ya shige dakin taron, zuwa yanzu ‘yan kwamitin gudanarwar jam’iyyar suna wani zama na sirri.

Advertisement

labarai