Connect with us

LABARAI

Dogara Na Shirin Karshe Na Sauya Sheka Duk Da Tattaunawarsa Da APC

Published

on

Kakakin Majalisar Wakilaiya, Mista Yakubu Dogara, na kan shirin daukan matakin ficewa daga APC gami da tsunduma cikin jam’iyyar PDP.
Jaridar Punch ta nakalto kan cewar ta gudanar da wani binciken da ke nuna mata Dogara babu wani muhimman lamari da ke nuni da cewar har yanzu Dogara na ci gaba da biyayya wa jam’iyyar APC, kana binciken ya gano cewar rade-radin da ke cewa Dogara na yunkurin shiga cikin jam’iyyar PDP babu tabbacinsa babu kuma wanda ya musanta.
Matsayar ta Dogara ta nuna a lokacin da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya fice daga APC makkonni kalilan da suka gabata, inda motsin Dogara ya yi likomo a lokacin da Saraki da tawagarsa ke sauya sheka.
Dogara bai halarci babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja ba, wanda kai tsaye wannan lamarin ma ke nuni da cewar akwai wata a kasa, ganin cewar babban taro ne wanda aka tattauna kan shirye-shiryen babban zaben 2019, kamatuwa yayi duk wani kusa a cikin jam’iyyar ya kasance a wajen taron sai aka duba babu fuskar Dogara a wajen ganawar ta masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC.
Sannan kuma bai halartar ganawar jam’iyyar a matakin Gunduma, karamar hukuma ko kuma tattaunawar jam’iyyar a matakin jiha, hakan ma kari ne kan shirin da ke tabbatar da Dogara bai wani tare da APC a halin yanzu.
Wakazalika, wasikar da mataimakin shugaban ma’aikatan Kakakin majalisar, Mista Cyril Maduabum, wacce ya aike wa shugaban jam’iyyar APC dangane da dalilan da suka sabbaba Yakubu Dogaran bai samu halartar babban taron ganawa na jam’iyyar da ya gudana a ranar Alhamis din ba.
Wasikar dai ta shaida cewar Dogara dai baya kasar Nijeriya, haka nan shi ma mataimakinsa Mr. Yussuff Lasun, shi ma baya nan.
Binciken nan ya ci gaba da gano cewar Kakakin majalisar na duba dacewa da kuma yanayin ficewarsa tasa ne, inda makusantansa suka tabbatar da cewar har yanzu Dogara na ci gaba da kallon lamura da kuma yadda zai yi wajen sauya sheka daga jam’iyyar.
Daya daga cikin makusantan Dogaran yake cewa, “batun sauya shekar Dogara ko rashin sauya shekarsa lokaci ne zai nunar hakan. Amma yanzu dai yana da dan sauran lokaci kan matakin da zai dauka walau a kujerar da ya ke nema ko akasin haka, sai dai tunani daban-daban, idan yana zurfafa tunaninsa kamar Saraki to ka ga dole ya dauki matakin hakan tun kafin lokaci ya kai ga kure masa, amma idan kuma ta kasa-kasa yake tunkara yana da sauran damar lokaci a garesa,” Inji makusancinsa
Wani makusanci kuma abokin Dogara, ya misalta cewar Kakakin majalisar na cikin ‘APC ne kawai a gangan jiki’, amma a ‘ruhinsa shi dan jam’iyyar PDP ne’.
Majiyarmu ya kara da cewa, “abun da ni na fahimta har yanzu Dogara na ci gaba da tattaunawa da APC kan yadda zai sake samun tikitin Kakakin Majalisa.
“muddin basu kai ga cimma matsaya ta fahimtar juna ba, la-shakka zai sanar da motsi na gaba,” Inji makusancinsa
A bayya ne yake, mazabar Kakakin majalisar tarayya, PDP ta yi gayar tasiri a cikinta, domin ko a zaben baya-bayan nan na cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu PDP ce ta samu gagarumar nasara a mazabar, inda kai karamar hukumar Bogoro PDP ta samu rinjaye.
Ya ce; “Idan ka duba wannan zaben ka san PDP tana da tasiri gaya a wajen mazabar Dogara, don haka da iyuwar hakan ma ya kara masa kwarin guiwar sauyawa.
“mutane da dama, daga abokansa da sauran masu bukatarsa, suna da muradin zabansa ne a karkashin jam’iyyar PDP,” Inji shi
Majiyarmu ta tuntubi mai magana da yawin Kakakin majalisar, Turaki Hassan, ba a samu wani bayani daga garesa kan wannan batun ba.
Kan batun rashin halartar Dogara wajen babban taron APC, Mai magana da yawun majalisar, Mr. Abdulrazak Namdas, ya shaida cewar Dogara ya tafi kasar Ingila a wannan lokacin na ganawar kusoshin jam’iyyar.
“Kakakin majalisa yana UK, akalla ina sane, idan yana kasa na sani idan ma bai kasar nan ina sane,” In ji shi
Kawo yanzu dai ido ya koma kan Dogara zai fice daga jam’iyyar hadi da shiga cikin jam’iyyar PDP ne ko kaka, inda masu kallon harkar siyasa ke ganin nan gaba kadan Dogara zai fito ya nuna sha’awarsa ta shiga PDP a sakamakon ababen da suka yi ta faru da kuma yadda ‘yar manuniyar siyasa ke nunawa a kan Kakakin majalisar ta tarayya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: