Aisha Seyoji" />

Dogon: Masu Nada Shugaba Ya Kwashe Wata Shida Ba Wanka, Ba Aski

A yau mun kewaya duniya inda muka ci karo da mutanen dogon
Filin namu na yau zai sada ku ne da mutanen kabilar dogon dake cibiyar plateu region dake Mali ta yammacin Africa, ta Kudancin lankwasar Nijar kusa da birnin Bandiagara, a Mopti Region. Yawan su ya kai kimanin 400,000 da 800,000, suna magana da yaren Dogo.
Rauhanai sun kasance ababe masu mutunci a wajen wadannan mutane, hakanne ma ya sanya suke danganta haihuwarsu ta ‘yan biyu da rauhanai, Nummo/Nommo Rauhanai ne mafiya muhimmanci wadanda mutanen kabilar su ka yi imani da shi, a yadda abin yake, su kan kwatanta Nummo su, su danganta shi sannan su yi masa lakabi da, maciji kadangare, hawainiya, saboda a cewar su su ne suke tafiya a hankali, a wasu lokutan kuwa su kan yi masa lakabi da kifi, wanda zai iya tafiya a kan kasa idan har bukatar hakan ta kasance, Tirkashi! Su dai Nummo su kan tashi ne tsaye a kan wutsiyarsu, jikinsu ya kasance kore shar. Sai dai kuma kamar yadda hawainiya ta kasance ta kan canja launi, su ma dai Nummo hakan yake kasancewa da su, su kan canza launi lokaci zuwa lokaci, har ya sanya a kance su kan canza zuwa dukkan kaloli na bakan gizo. Wani lokacin kuma su kan yi masa lakabi da Ruhu na cikin ruwa
A wani lokacin can baya, mutanen kabilar sun yi fama da matsalar haihuwar irin ta ‘yan biyu, ko kuma dai daya ko kuwa haihuwar ta kasance mace, sannan kuma namiji a lokaci daya wanda ya zamto babbar barazana a garesu a wancan lokaci.
Al’ada irin ta kaciya ta samo asali ne tsakanin wadannan mutanen bayan an karewa da Nummo suka yi da cewar a wannan lokacin fa an kai matsayin da haihuwar mata da maza yana kokarin kwace haihuwa gaba ki daya, musamman ma na ‘yan biyu, a halin da ake ciki shi ne, a maimakon mace ta haifi ‘yan biyu sai dai ta haifi daya, sannan kuma dayan zai kasance mai dauke da halittar mace da kuma namiji a lokaci daya. Ganin hakan ne ya sanya mutanen kabilar suka bai wa kaciya muhimmanci sosai, domin a cewar su, kaciya ita ce kadai hanyar da za ta yi masu maganin wannan al’amari, a cewar su namiji ya zama namiji, yayin da mace kuma ya kamata ta tsaya a matsayinta na mace, hakan ne ya sanya idan an yi haihuwar jaririn da ya kasance mai halitta biyu sai a yi amfani da hanyar kaciya domin barin sa a matsayin yaro kawai.
A yanzu haihuwar ‘yan biyu ta zamto abin murna da farin ciki wanda ake yi wa gagarumin biki domin a cewarsu haihuwar ‘yan biyu yana sanya wa a tuna lokacin da aka hallicci dukkan mutane a matsayin ‘yan biyu.
Zamantakewa
Gidaje da kuma al’ummar dogon suna zama ne a karkashin kulawar namijin da ya kasance babba ,wanda ya kasance shi ne da na fari ga mai gidan ko mai unguwar ko kuwa a ce mai gunduma.
Mutanen dogon mutane ne da suka tashi cikin soyayya, shakuwa, da amincin juna. Misali akwai wata hadaya wacce tafi kowanne hada muhimmanci a wajensu wacce mata za su yi ta ya bawa mazaje, yayin da kuma mazan za su yi ta yi wa mata godiya, yara su kan nuna yabawar su ga tsofaffi, sannan kuma tsofaffin su kan yaba da gudunmawar kananan, akwai wata al’ada kuma ta gaisuwa, inda duk inda dan kabilar dogon ya hadu da dan uwansa za su yi dogiuwar gaisuwa, ta hanyar yi wa shi wanda ake yi wa gaisuwar tambayoyi, yayin da shi kuma zai ba da amsa da ‘Sewa’ ma’ana kowa da komai lfy
Hogon
Hogon shi ne ya kasance Shugaba Rauhani na kauye, tsofaffi daga cikin kabilar suke da alhakin zaben hogon bayan an zabe shi kuwa zai kasance mai a matsayin wanda ake nadawa har na tsawon wata shida tsawon wannan lokaci ba’a yarje masa ya yi wanka ko aski ba, zai kasance a cikin fararen tufafi, sannan kuma ba’a yarda wani ya tabashi ba. A kan sami yarinya karama wacce ba ta fara al’ada ba ita ce wacce za ta rika kula da shi, kamar ta bangaren gyaran gida da kuma yi masa abinci, daga bisani ta koma gidan iyayenta yayin da dare ya yi, bayan wannan lokaci zai sanya jan kaya, sannan da abin hannu wanda yake dauke da duwarwatsu masu muhimmanci wanda ke nuna girmansa, daga nan kuma sai a musanya wannan yarinya da take yi masa hidima da daya daga cikin matansa, wanda ita ma bayan ta gama masa hidima za ta koma gidansu. Hogon zai kasance shi kadai a gidansa yayinda yayi imani da cewa Macijinsu mai tsarki mai su na ‘Lebe’ ya kan zo cikin dare domin tsarkake shi domin koya masa hikima.
Aure
Auren mace daya shi ne aure da ya fi tasiri ga mutanen kabilar, kuma ake koyi da shi, duk da kasancewa namiji yana da damar ya auri mata biyu kawai, namiji ba shi damar auren mace fiye da daya, mafi akasari auren fari ya kan kasance aure ne irin na hadi, ma’ana iyaye ne su kan duba wanda ya dace su hada su aure, wanda za su yi aure na biyu su ne suke da damar zabin mace ko miji ga mace. Auratayya na faruwa tsakanin mutanen kabilar, akan yi aure kuma tsakanin ‘yan uwan juna ko kuwa a auro wata ko wani daga wata kabilar ta daban.
Mutanen kabilar ba su yarda macen da ta fito daga kabilar ta auri gursumeti ba (gold smith)
Bayan an daure aure kuwa mace za ta ci gaba da zama ne a gidan iyayenta har zuwa lokacinda za ta yi haihuwar fari, yayin da miji zai ci gaba da zama a gidansa na gwauranta wanda zai kasance gidan da ya rayu a ciki tun daga shekara takwas zuwa goma, bayan mace ta yi haihuwar fari ne, kuma sai su tattara ita da mijin da abinda aka haifa zuwa wani gida wanda gidan zai kasance a kauyensu mijin, ya halatta a yi saki, kuma yayin da mace ta rabu da mijinta tana da damar daukar dan karamin danta ne kadai domin tafiya da shi inda za ta bar sauran a gidan mijinta wato mahaifinsu ko iyayensa.
Gado
Yayin da mai gida ya mutu kaninsa shi ne a layin farko na gado, sai na biyunsa kuma babban daga mamacin, a wani bangaren kuma gado ya kan tafi hannun babban da ga mamaci, domin shi ne zai ci gaba da kula da ‘yan uwansa,sai kuma kanin mamacin ya zo a layi na biyu, idan kuwa mace ce ta rasu gado zai fara zuwa ne wajen ‘yarta babba mace, sai kuma kanwarta mace ta zo a ta biyu.
Addini
Su kan yi koyi da addinin gargajiya, yayin da a yanzu kuma wasun su suna koyi da addinin musulunci da kuma addinin kiristanci.

Exit mobile version