Daga Ibrahim Muhammad,
Dokajin Sarkin Gaya, Hakimin Wudil, Alhaji Muhammad ya nada Ambasada Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya a matsayin Marafan Dokajin Hakimin Wudil a fadarsa Ranar Asabar da ta gabata.
Nadin, wanda ya hada da na wasu mutum uku da aka yi, na Wali da Sa’i da Sarkin Larabawan Wudil, ya sami halartar dimbin jama’a daga sassa da dama daga ciki da wajen Kano.
Hakimin na Wudil, Alhaji Abba Muhammad ya yi kira ga wadanda aka nada su rike wannan nauyi da Allah ya ba su wajen hada kan al’umma da bunkasa ci gaban Wudil da masarautar Gaya.
Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida bayan nadin da aka yi masa na Marafan Dokajin Hakimin Wudil Ambasada Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya ya bayyana cewa wannan nadi da aka yi masa ran Asabar 3/4/2021 kyakkyawan rana ce da ba zai manta da ita ba, wanda aka yi masa abin da bai za ta bai tsammani ba, saboda ni’imar Allah.
Ya ce tsakaninsu da Allah sai godiya sun halarci garin Wudil a karkashin masarautar Gaya any i masa nadin Marafa, don haka duk wanda Allah ya yi wa ni’ima, to ya gode masa domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ambasada Yusuf Wakilin Dukiya ya yi nuni da cewa an yi musu wannan sarauta ne ba don sun isa ba, sai don yardar Allah da amincewarsa. Shi ya ba su wannan dama na kula da jama’a da kasar Dokaji suna yi wa Allah godiya.
Ya ce, kuma a matsayinsa na wanda ya sami sarautar Marafan Dokajin Hakimin Wudil, yana gode wa jama’a bisa amsa kira da suka yi na halartar wajen ‘yan uwa da abokan arziki sun nuna halasci da kauna Allah ya saka musu da alkhairi.
A nasa jawabin, Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya ya ce aikin Dokaji shi ne kulawa da garin, Dokaji kuma suna cikin masarautar Gaya kuma ba sai an musu tsawa an ce su kula ba domin wajibi ne su kula domin kamar gidan su ne aka ce su share a wanke shi, nasu ne dama shi ya sa suke bukatar a tayasu da addu’a dan Allah ne zai iya musu.
Wakilin Dukiya Ambasadan Zaman lafiya Marafan Dokaji Alhaji Yusuf Ibrahim ya ce mai sonka da kaunarka ba abin da ba zai iya yi maka ba Shi ya sa Dokajin Sarkin Gaya Alhaji Abba ba zai iya fadar kaunar da ke tsakaninsu da shi ba tunda sun tashi suna son juna kuma dama sai an samu wani ke baiwa wani.
Ya ce duk mutanenda akayi musu sarauta ya zabi mutane na kwarai, bai yi na tumun dare ba, shi ya sa a taya Hakimi da addu’a, su kuma su dora akan abin da Allah ya ba su iko.
Shi kuwa Anas Yusuf Wakilin Dukiya cewa ya yi mahaifinsu Mutum ne mai jama’a sosai, shi ya sa mutane suka taru sosai a nadin nasa saboda yana zaune lafiya da jama’a a duk inda yake.