Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Dokar Amurka Kan HK Ta Nuna Yunkurinta Na Tayar Da Tarzoma A Yankin

Published

on

Kwanan baya majalisar dattijai ta kasar Amurka ta zartas da wata doka kan ‘yancin yankin Hong Kong na kasar Sin, inda aka yi kashedin cewa, Amurka za ta yi wa wadanda za su lahanta ‘yancin Hong Kong takunkumi, misali mutane ko hukumomin kudi ko kamfanoni, matakin da ta dauka tsoma baki ne a fili cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma ya take babbar ka’idar dokokin kasa da kasa da huldar dake tsakanin kasa da kasa, har ya nuna makarkashiyar wasu ‘yan siyasar Amurka ta tayar da tarzoma a yankin Hong Kong, a sanadin haka al’ummun kasa da kasa sun suka kan matakin.

Tun bayan da masu yunkurin neman ‘yancin Hong Kong suka kaddamar da zanga-zanga bisa fakewar gyara doka kan masu laifuffuka da suka tsira a watan Yunin bara, sai masu tayar da tarzoma suka fara kai hari ga hukumomin jama’a karkashin goyon bayan wasu kungiyoyin dake ketare, lamarin da ya kai ga lalata motoci da gine-gine, har wasu mazauna yankin sun rasa rayuka ko jin rauni, duk wadannan sun kawo barazana mai tsanani ga moriyar kasar Sin da tsaron kasar baki daya. Ba zai yiwu a yi biris da laifuffukan cikin wata kasa mai doka da oda ba, kamar yadda tsohon shugaban hukumar manufar tattalin arziki da kasuwanci ta kasar Birtaniya John Ross ya bayyana, babu wata kasa da za ta amince da laifuffuka, don haka kasar Sin tana da hakkin fitar da dokar tsaron kasa, domin harka ce ta cikin gidan kasar Sin.
An lura cewa, kafa dokar tsaron kasa zai kara kyautata manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” ta gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, amma wasu ‘yan siyasar Amurka sun musunta hakan da gangan, wato sun canja ma’anar gudanar da harkokin yankin karkashin jagorancin gwamnatin tsakiyar kasar Sin zuwa ma’anar ‘yancin kai, manufarsu ita ce tayar da tarzoma a yankin Hong Kong.
Hakika gwamnatin tsakiyar kasar Sin tana sauke nauyin dake wuyanta yayin da take goyon bayan gwamnatin yankin Hong Kong, saboda ba ta aiwatar da dokokin kiyaye tsaron kasa da babban yankin kasar ke amfani da su a yankin Hong Kong kai tsaye ba, sai dai ta sake tsara wata sabuwar dokar tsaron kasa a yankin, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin tsakiyar kasar Sin tana mutunta manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu”.
Ko shakka babu matakin da Amurka ta dauka ba shi da ma’ana ko kadan, al’ummun kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400, ciki har da mazauna yankin Hong Kong za su tsai da kuduri kan makomarsu, ya dace ‘yan siyasar Amurka su daina tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: