Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Dokar Amurka ta Xinjiang: Shisshigin Amurka Yana Shan Suka

Published

on

Tun bayan da kasar Amurka ta yi gaban kanta bisa ra’ayin son zuciya da neman boye laifukanta tana hangen na wasu, har ma ta yi yunkurin samar da kudurin dokar da ta kira “Uyghur Human Rights Act of 2020” wato dokar “Kare hakkin al’ummar Uyghur ta 2020”, wannan mataki da ta dauka ya janyo mata suka daga kwararrun masana da jami’an diflomasiyyar kasa da kasa inda suke ganin baikenta kasancewar kasar ta zama abin da ake kira gwano wato ba ta jin warin jikinta. Kwararru sun yi Allah wadai da dokar Amurka kan yankin Xinjiang sun bayyana matakin a matsayin shiga harkokin cikin gidan Sin, kuma wannan mataki ya ci karo da yarjejeniyar MDD, kana ya saba dokokin kasa da kasa na ’yancin ikon da kasar Sin ke da shi kan yankunanta. Masu sharhi kan al’amurran siyasar kasa da kasa irin su farfesa Andrei Manoilo, na fannin nazarin kimiyyar siyasa na jami’ar jihar Moscow, yana ganin cewa, Amurka tana daukar kasar Sin a matsayin wata babbar abokiyar takararta ne kuma ta jima tana yunkurin neman hanyar da za ta haifarwa kasar koma baya da kuma shafa mata kashin kaza. Hakika wannan yunkuri na Amurka ba zai haifar mata da da mai ido ba sai dai ma ya kara nunawa duniya irin gazawar da kasar ke da shi a idon kasa da kasa. A bayyane take a fili, yayin da kasar Sin take ta kokarin yaki da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi, kasar Amurka tana ta kokarin yiwa aikin yaki da ta’addancin da matakan kandagarkin da Sin ke dauka gurguwar fassara inda take nuna matakan na kasar Sin a matsayin take hakkin bil adama. To wai shin ko babatun da Amurka ke yi game da batun yaki da ta’addanci ga duniya yaudara ce? Ko kuma tana amfani da kalmar yaki da ta’addanci ne domin cimma wata manufarta? Lallai biri ya yi kama da mutum, domin kuwa idan har Amurka da gaske take yi game da ikirarinta na yaki da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi to banga dalilin da za ta kwayewa wata kasa baya ba a bisa kokarin yaki da ta’addancin. Wata kila dai akwai wata makarkashiya. Mai yiwuwa ne amsar wadancan tambayoyi na sama za su iya fitowa fili cikin kalaman Peter Kagwanja, shugaban cibiyar tsara manufofin Afrika na kasar Kenya, inda masanin na Afrika ya bayyana cewa, “a koda yaushe Amurka tana amfani da kalmar hakkin dan adam a matsayin wani makami wanda take kaddamar da hari kan abokan hamayyarta”. Koma dai mene ne manufofin gwamnatin Sin ya saba da ikirarin da Amurka ke yi, domin kuwa, har kullum kasar Sin tana dora muhimmanci kan batun hada kan al’ummar kananan kabilunta da bunakasa ci gaban al’adun kabilu daban daban, kuma matakan da kasar ke dauka game da batun yaki da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi yana haifar da kyawawan sakamako. Ta yaya za’a ce kasar dake bayyana kanta a matsayin mai rajin kare hakkin dan adam a duniya, amma ta rufe idonta kan muhimman batutuwan da suka shafi nuna wariyar launin fata da take hakkin bil adama, da aikata kisan gilla kan bakaken fata dake ta faruwa a cikin kasarta. Alal misali kamar abin da ya faru kwanan nan na kisan gillar da ’yan sandan Amurka fararen fata suka yiwa Ba’amurken nan bakar fata, lamarin da ya haifar da zazzafar zanga-zanga a fadin duniya. Lallai Amurka ta zama gwano ba ta jin warin jikinta musamman saboda yadda kasar ke hayewa kan kololuwar laifukanta amma tana hangen na wasu. Kuma a wasu lokutan ma, tana tsayawa kai da fata wajen kirkirar sharri kan sauran kasashen duniya. Alal misali batun kudurin dokar da Amurka ta sanyawa hannu kwanan nan kan jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ta kasar Sin, kwararrun masanan kasa da kasa da dama sun yi tsokaci tare da yin Allah wadai gami da sukar manufofin Amurkar kan wannan batu wanda suka bayyana karara cewa dokar ta saba yarjejeniyar MDD, sannan ta ci karo da hakikanin ’yancin da kasar Sin ke da shi na yin iko da yankunanta. Wannan kudurin doka dai haramtacce ne, saboda gwamnatin Amurka ko kuma majalisar wakilan kasar, ba su da ikon zartar da kowane irin kudurin dokar da za’a aiwatar da shi a wasu kasashen duniya. Lallai ya kamata mahukuntan Washington su dinga sara suna duban bakin gatari domin idan an ki ji ba a ki gani ba. (Marubuci: Ahmad Fagam daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: