Rabiu Ali Idabawa" />

Dokar Hana Fita Ta Fara Aiki A Lardunan Accra Da Kumasi Na Ghana

Gwamnatin kasar Ghana ta haramta zirga-zirga a yankuna biyu mafi girma a kasar daga wannan litinin,

domin dakile yaduwar cutar COBID-19 da ke ci gaba da halllaka jama’a a kasashen duniya.

 

Shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya ce daukar matakin ya biyo bayan samun mutane 137 da suka

kamu da cutar, yayin da tuni 4 suka rasa rayukansu.

 

Akufo-Addo ya bayyana yankunan da suka hada da Accra da kuma Kumasi, to sai dai ya ce matakin bai

hana mutane fita domin sayen abinci da ruwan sha da magunguna ba, ko kuma amfani da ban dakin

jama’a.

Shugaban ya ce dokar ta makwanni biyu ta haramta zirga zirgar jama’a daga gari zuwa gari a mota da

jiragen sama, sai dai wadanda jami’an kula da lafiya ke aiki da su kawai.

 

Tuni Ghana ta bi sahun kasashen duniya wajen rufe makarantu da dakatar da ayyukan gwamnati da

kuma hana taron jama’a.

Exit mobile version