Yusuf Shuaibu" />

Dokar ‘Social Media’: Ba-gudu-ba-ja-da-baya, In Ji Gwamnatin Tarayya

Dokar ‘Social Media’

Gwamnatin tarayya ta kara kare matsayinta na ci gaba da samar da tsarin da zai daidaita ayyukan kafafen sadarwa na zamani da jama’a ke walwala a cikinsu.

Ta bayyana cewa, hakan yana da matukar mahimmanci wajen dakile labarun karya, domin su ne suka yi tasiri wajen hargitsa lamura a kasar nan lokacin zanga- zangar ENDSARS.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana hakan a jiya. Ya kara da cewa, wasu bata-gari sun yi amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen sace wasu kayayyaki.

“Mun gudanar da ganganmin yaki da labarai marasa inganci tun a shekarar 2018. Gaskiyar magana ita ce, mun fadakar da illolin yada jita-jita da labaran karya da abubuwan da suke haddasawa a cikin kasar nan. Mun gabatar da dukkan matsalolin da ake samu a wajen gangaminmu.

“Ana amfani da kafafen sadarwar na zamani wajen tada zaune tsaye wanda zai kai ga lalata kayayyakin gwamnati da masu zaman kansu. An ga yadda ake nuna hotunan mutane ciki har da wadanda ake zargin sojoji sun kashe a Lekki Toll Gate, wanda hakan ya kara rura wutar zanga- zanga har daga karshe ya koma tashin hankali.

“Kamar yadda muke fadi a kullum, gwamnati ba za ta zura ido tana kallon ana abubuwan da su dace ba a cikin kafafen yada labarai na zamani.

“Mun mayar da hankalinmu ne wajen dakile labaran karya wanda a yanzu gwamnatin tarayya take shirin rufe wasu kafafen yada labarai. Amma ba ma shirin rufe kafafen yada labarai gabadaya.

“A kullum muna samun shawarwari a kan abin da ya fi dacewa mu yi, yanzu dai za mu kayyade ayyukan kafafen sadarwa na zamani. Domin Nijeriya ba za ta taba lamuntar yada labarum kanzon kurege ba,” in ji shi.

Exit mobile version