CRI Hausa" />

Dole A Kara Karfafa Hada Kai Tsakanin Kasa Da Kasa Yayin Raya Cinikin Hidima

Kwanan baya kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta fitar da rahoton cinikin duniya na shekarar 2019 a Geneva, inda aka yi nuni da cewa, yanzu cinikin hidima yana taka rawar gani a harkokin cinikin duniya, inda ya kai kaso sama da 20 bisa dari, amma a shekarar 1970 kaso 9 bisa dari ne kawai, ana ganin cewa, a cikin shekaru sama da goma masu zuwa, cinikin hidima zai kara ba da gudumowa a harkokin cinikin duniya, a don haka dole ne kasashen duniya su kara hada kai ta yadda za a kara habaka cinikin hidima.
Idan ana son kara karfafa hadin gwiwar ciniki a tsakanin kasa da kasa, abu mafi muhimmanci shi ne a kawar da abubuwan dake kawo cikas ga cinikin hidima, a matsayinta na babbar kasa mai sauke nauyi bisa wuyanta, har kullum kasar Sin tana kokari matuka domin kawar da irin wannan shinge, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu babban sakamako a bangaren bude kofa ga kasashen ketare yayin da take gudanar da hada-hadar kudi, kawo yanzu ta riga ta kara bude kofa ga ketare a fannin harkokin banki da hada-hadar kudi da kuma inshora, a shekara mai zuwa ma za ta kara habaka kasuwar daga duk fannoni.
Kana idan ana son kara karfafa hadin gwiwar ciniki a tsakanin kasa da kasa, ya dace a kafa sabon dandali, misali kasar Sin ta himmatu kan hadin gwiwar cinikin hidima tsakaninta da kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, inda adadin kudin da ta samu yayin da take gudanar da hadin gwiwa da wadannan kasashe a shekarar 2018 ya kai dala biliyan 121.7, adadin da ya kai kaso 15.4 bisa dari cikin daukacin cinikin hidimar kasar ta Sin.
A halin yanzu tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba cikin lumana ba, don haka kamata ya yi kasashen duniya su kara fahimtar babban karfi a asirce na cinikin hidima, su hada kai domin kawar da abubuwan dake kawo cikas ga harkokin ciniki tare da ingiza ci gaban cinikin hidima a fadin duniya.

(Mai Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version