Daga Zubairu M Lawal,
Gwamnatin Najeriya da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun cimma matsaya da kuma himmatuwa dan ganin an kawo canji na gaske a fannin abinci.
Najeriya tana aiki tukuru tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya da kuma wasu masu fada aji na kasar dan ganin an shawo kan matsalar abinci a kasar da kuma samar da abinci mai gina jiki kasar .
Mai lura da sashen tsarin abinci na majalisara dinkin duniya da kuma tsare tsare, Misis Olusola Idowu a tattaunawa da tayi da yan jaridu,
Misis Idowu tace taron tsarin abinci za’a gudanar dashine a fadin kasar sannan kuma akwai gudummawa wanda shi zai taimaka wajen dakile matsalar abinci a kasar baki daya.
Ta kara da cewa a yayin da muke samun karuwan mutane a kasar ya kamata ace anyi tsari sosai don kaucewa fadawa yunwa da fatara. Saboda yawan al’umman Nijeriya yafi karfin abincin da suke amfani dashi. Dole a samar da sabuwar tsarin yadda za a kaucewa rayuwan yunwa a Nijeriya.
Mista Edward Kallon Babban kodineta na Majalisar Dinkin Duniya a tarayyar Nijeriya, shima ya kara da cewa lallai tsarin abinci abune mai amfani ganin yadda muke samun karuwan mutane kullum, shine hanyar da za’abi dan ganin an kauce wa fadawa cikin halin ka’in-dana’i.
Burinmu shine mu ga an cigaba da tattaunawa da kuma bada hanyoyin da za a bi dan ganin cewa an samar da hanya sosai na tsarin abinci mai inganci a fadin Nijeriya, ta yadda al’umman kasar za su yi walwala gami da jin dadin rayuwa.
Ya kara da cewa wajibine a kaucewa matsalolin yaunwa saboda yunwa babban tashin hankali ne, yana kuma haifar da matsaloli daban-daban.