Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Dole A Yiwa Ozil Hakuri – Zidane

by Abba Ibrahim Wada
January 17, 2021
in WASANNI
3 min read
ozil
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce dole a yi hakuri da dan wasan kungiyar, Eden Hazard, bayan da ya kasa tabuka wani abun kirki a wasan kusa da na karshe na gasar Supercopa de Espana da kungiyar Athletico Bilbao suka doke su daci 2-1 a daren Alhamis din data gabata.

Kwallaye biyu a zubin farko na wasan daga Raul Garcia suka kai Bilbao wasan karshe inda za su gwabza da kungiyar Barcelona, duk da cewa dan wasa Karim Benzema ya zura kwallo daya a raga a minti na 73 na wasan amma duk da haka basu iya farke ragowar kwallon ba.

Sau daya Hazard ya buga kwallon da ta nufi wajen mai tsaro raga kafin a cire shi a tsakiyar wasan, aka maye gurbinsa da Binicius Junior mai shekaru 20 wanda kuma daga shgarsa filin ya buga wasa mai kyau sama da wnada Hazard din ya buga.

Hazard dan kasar Belgium ya yi ta fama da jinyar rauni tun da ya koma Real Madrid, kuma kwallaye biyu kawai ya ci daga wasanni 10 a dukkan gasanni a wannan kaka sai dai har yanzu Zidane yana ganin dan wasan zai warware nan gaba.

Zidane ya ce dan wasan mai shekaru 30 yana bukatar lokaci domin dawowa kan ganiyarsa, yana mai watsi da batun da ake cewa magoya baayan Real Madrid sun gaji da rashin katabus dinsa kuma sun fara nuna damuwarsu a kansa.

Sai dai bayan tashi daga wasan kuma Zidane ya bayyana cewa ‘yan wasa da masu koyarwa basu da abinda zasu gayawa masu saurare da magoya bayan kungiyar sakamakon rashin nasarar da sukayi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Atletico Bilbao a wasan dab dana karshe din a gasar Spanish Super Cup na wannan shekarar.

Daman dai karawa tsakanin Real Madrid da Athletic Bilbao mai dadadden tarihi ce tun lokacin da aka fara wasannin gasar kwallon kafa a kasar Spaniya sai dai kuma wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu  suka fafata a Spanish Super Cup.

Shi wannan Supercopa an fara buga shi a shekarar 1982 kuma Athletic Bilbao ce ta fara lashe shi, bayan da ta lashe gasar La liga da kuma Copa del Rey a kakar wasan guda daya a wancan loakci.

A shekarar 1902 a wani kofi da aka sa don bikin taya Alfonso na bakwai murnar sarauta, kuniyoyin biyu sun shiga gasar, amma basu hadu a tsakaninsu ba  amma kuma da fara gasar Copa del Rey a Spaniya Aathletic ta hadu da Real Madrid ta kuma yi nasara a wasan karshe da ci 3-2.

Real Madrid ta yi nasara a kan Athletic da ci 3-1 a wasan La Liga ta bana ranar 15 ga watan Disamba sannan Real Madrid ce ke rike da kofin da ta lashe a Saudi Arabia, bayan da ta yi nasara a kan Atletico Madrid kuma shi ne Spanish Super Cup na farko da aka buga ba a cikin Spaniya ba.

Ranar Laraba Barcelona ta kai zagayen karshe, bayan da ta yi nasara a kan Real Sociedad da ci 3-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasa 1-1 kuma Barcelona ce kan gaba wajen yawan lashe kofin mai 13 jumulla, ita kuwa Real Madrid guda 11 ne da ita, yayin da Athletic Bilbao take da shi guda biyu.

Sai dai bayan tashi daga wasan mai koyarwa Zidane ya bayyana cewa basu da abinda za su gayawa masu kallonsu da magoya bayansu saboda basu buga wasa yadda yakamata ba kuma akwai sauran aikin a gaban ‘yan wasan idan har suna son su lashe kofi a wannan kakar.

“A minti 45 na farkon wasan bamu buga wasa yadda yakamata ba saboda bamu fara buga wasan da kyau ba sannan kuma suka zura mana kwallaye biyu a raga wanda abune mai wahala a irin wannan gasa” in ji Zidane

Ya ci gaba da cewa “Munyi kokari bayan an dawo daga hutun rabin lokaci amma duk da haka kokarin mu bai kai yadda nayi tunani ba duk da cewa mun zura kwallo daya amma yakamata ace mun zura sama da daya.

Kawo yanzu dai Barcelona zata kece raini da Atletico Bilbao a wasan karshe na gasar a yau ya yinda Real Madrid kuma zata bari har sa ranar Laraba mai zuwa sannan ta buga wasa da kungiyar Alcoyano a gasar Copa Del Rey ta bana.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ronney Ya Yi Ritaya Daga Buga Kwallo Kuma Ya Zama Cikakken Mai Koyarwa

Next Post

Ban Damu Da Jita-Jitar Korata Daga Manchester United Ba, Cewar Solkjaer

RelatedPosts

Arteta

Arteta Ya Mayarwa Da Paul Merson Martani

by Abba Ibrahim Wada
19 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya mayarwa...

Tuchel

Kowane Wasa A Ingila Mai Wahala Ne –Thomas Tuchel

by Abba Ibrahim Wada
19 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel, ya bayyana...

Alaba

Real Madrid Tana Cigaba Ta Tattaunawa Da Alaba

by Abba Ibrahim Wada
19 hours ago
0

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa...

Next Post
Solkjaer

Ban Damu Da Jita-Jitar Korata Daga Manchester United Ba, Cewar Solkjaer

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version