Connect with us

RA'AYINMU

Dole APC  Ta Yi Zaben ’Yar Tinke A Bauchi – Kaftin

Published

on

A shekaranjiya ne dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Kaftin Bala Jibrin da Sanata Ibrahim Yakubu Lame suka hada kansu wuri guda inda suka shelanta cewar adalci shi ne jam’iyyarsu ta APC ta yi zaben fitar da gwani ta hanyar amfani da ‘yar tinke domin shi ne kawai zai ba su zarafin kwace mulki daga hanun gwamna mai ci.

‘Yan takarar sun  bayyana hakan ne a lokacin da suka kai kansu ga uwar jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, inda suka jaddada bukatar a yi musu amfani da zabe ta hanyar ‘yan tinke.

‘Yan takarar sun gargadi jam’iyyar APC reshen jihar da kada ta sanya son rai da son zuciya wajen zaben fitar da gwani, sannan kuma sun yi watsi da batun tsai da mutun daya tilo a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Lame da Kaftin sun shaida wa uwar jam’iyyar cewar sun cire kudade har miliyan ashirin da biyar kowannensu domin yankar fom din tsayawa takara, suna neman jam’iyyar APC ta yi watsi da batun amfani da delegates domin shi ne zai kai su ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Da yake nasa jawabin, Kaftin Muhammad Bala Jibrin ya shaida cewar ya biya kudin sayen fom ne domin yana da muradin sabunta jihar Bauchi, a bisa haka ne ya shaida cewar za su hada karfi da Lame domin kwatar mulki daga hanun gwamna mai ci.

Ta bakinsa, “sanin kowa ne a kasa an ce duk da cewa jihohin da suke da wasu hujjoji na musamman za su zauna da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kuma ‘yan takara a yanke hukunci kan mene ne za a yi. walau ‘yar tinke ko akasinsa,” In ji shi

Ya nuna fushinsa kan rashin sanya shi cikin masu ruwa da tsaki da aka yi kan fitar da matsaya kan yin amfani da delegates ko ‘yar tinke wanda jam’iyyar reshen jihar Bauchi ta cim ma matsaya kan za su yi amfani da delegates ne.

Kaftil Bala Jibrin, ya shaida cewar zaben ‘yar tinke za a yi musu a jihar Bauchi ba wani rufa-rufa ba, “saboda haka mun zo mu fadi wa jam’iyya ta kasa, mu kuma fada wa jam’iyya a matakin jihar Bauchi cewar abin da gwamnatin tarayya ta ce na ‘yar tinke, shi din nan za a yi mana a jihar Bauchi.

“Domin na farko akwai kesa-kesai har guda biyu a kotu. Akwai kara da dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Alhaji Shehu Sanin Malam ya shigar, akwai na biyu kuma, mu kusan mutum goma muma mun shigar da tamu karar na cewar ba a yi mana adalci ba wajen zaben fitar da jagororin jam’iyya da aka gudanar a kwanakin baya,” A cewar Bala Jibrin

Ya daura da cewa dokar kasa ta fayyace yadda za a yi a dukkanin jihar da suke da wani korafi a kotu, “dokar kasa ta ce duk inda ake da kara na rigima ma ba za a yi amfani da delegates, ‘indirect’ ba. balle tamu karar har ta je gaban Alkali, ina tasirin a yi zabe da delegates din da bayan sati biyu idan kotu ta ce su rusa su ne duk abin da suka yi a baya ya rushe?. Maganin kowace matsala a jihar Bauchi ne a yi ‘yar tinke kawai,” Kamar yadda yake bayyanawa

Dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar ya bayyana cewar za su hada karfi da sauran ‘yan takarar domin kwace mulki daga hanun gwamna mai ci.

Bala Jibrin ya kara da cewar dole ne su tashi tsaye domin kare martaba da kuma kimar jihar Bauchi, yana mai bayyana cewar jihar Bauchi ta kasance jiha marar ci gaba da walwala duk da samun maguden kudade da jihar ke samu.

Shi ma abokin takararsa a jam’iyyar ta APC, Sanata Ibrahim Yakubu Lame, ya shaida cewar a shirye suke su kwace mulki daga hanun gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar, “mun zo nan ne domin mu shaida wa jam’iyyar APC mun yanki katin tsayawa takarar a karkashin APC kuma mun biya kudinmu. Muna kuma son mu sanar muku cewar APC jam’iyyace wacce ta yarda da demokradiyya,” Kamar yadda ya fadi

Lame ya daura da cewa, alakar da ke tsakaninsa da dan uwansa Kaftin Bala Jibirin zai kai su ga samun gagarumar nasara na kwace mulki, ya kuma bayyana cewar dole ne APC ta kasance mai gudanar da adalci a cikin lamarinta domin wanzuwar zaman lafiya.

“Ka’idar jam’iyya ba son kan wani ko nuna wariya ga wani shi ne zai ba ku shugabanci ba; abin da nake cewa shi ne a jam’iyyar APC wanda mune muka ginata muka kawo ta jihar Bauchi kuma yau a zo a maishe mu saniyar ware ba.

Lame ya shaida cewar mutanen jihar Bauchi sune neman maceci, don haka sun tashi tsaye domin tabbatar da wannan ga jama’an jihar Bauchi, ya bayyana cewar za su hada kansu domin ceto jihar Bauchi.

Yake muku cewa, “Hanya daya da jama’a za su yarda an yi musu adalci shi ne a yi’yar tinke, mu shi muke so a jihar Bauchi domin wanzar da adalci,” In ji dan takarar gwamna a jam’iyyar APC

Da yake maida jawabi a madadin uwar jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, mukaddashin shugaban jam’iyyar, Muhammad Hassan Tilde ya shaida cewar sun yi gayar farin ciki a bisa ganin ‘yan takara biyu kansu a hade.

Ya kuma shaida cewar za su yi adalci wa dukkanin ‘yan takara a kowani lokaci, dangane da wasu korafe-korafen da ‘yan takarar suka gabatar kuwa, ya bayyana cewar dokar jam’iyyar APC ya fayyace yadda abubuwa da dama za su tafi, don haka ya nemi kowani dan takara a mutunta dokar jam’iyyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: