Connect with us

WASANNI

Dole Chelsea Da United Su Biya Fam Miliyan 90 Kan Havertz

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Liberkusen ta bayyana cewa dole sai kungiyoyin Manchester United da Chelsea sun biya fam miliyan 90 idan har suna son sayan dan wasan kungiyar, Kai Havertz, wanda tauraruwarsa take haskawa a halin yanzu.

Matashin dan wasan dai yaja hankalin manyan kungiyoyi da dama a duniya wanda hakan yasa kungiyar da yake bugawa wasa ta bayyana cewa bata da niyyar sayar dashi a wannan kakar duk da cewa dan wasan yana fatan tafiya daya daga cikin manyan kungiyoyin da suke bibiyarsa.

Tun farkon fara wannan kakar aka fara jita-jitar cewa dan wasan zai koma daya daga cikin manyan kungiyoyin duniya saboda yadda tauraruwarsa take haskawa a duniya tun yana matashin yaro.

Dan wasa Havertz, shine dan wasa na farko a tarihin ‘yan wasan kasar Jamus mai shekara 20 a duniya daya zura kwallaye 35 ba tare da ya kai shekara 21 ba a duniya hakan yasa ake ganin nan gaba zai zama babban dan wasan gaba mai zura kwallo a raga anan gaba.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen tana fatan doke kungiyoyin Real Madrid da Manchester United da Chelsea wajen sayan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Liberkusen, Kai Havertz.

Sai dai rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa gaba daya kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan zasu iya rasa dan wasan saboda kudin da Liberkusen din ta sakawa dan wasan a wannan yanayin da annobar cutar Korona ta addabi duniya.

An tabbatar da cewa wakilin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, mai kula da sayo ‘yan wasa ya shirya Magana da Bayer Liberkusen akan dan wasan sai dai kungiyar ba za ta wuce fam miliyan 75 ba idan har za’a iya sayar mata.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Liberkusen ta bayyana cewa dan wasan bana sayarwa bane Sai dai dan wasan yana da ragowar kwantiragin shekara biyu a kungiyarsa tasa hakan yasa ake ganin kungiyar zata nemi kudi kusan fam miliyan 80 ga duk kungiyar da zata iya sayansa a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bana da za a bude anan gaba kadan.

Kungiyoyin Chelsea da Liberpool ne dai suke bibiyar dan wasan sai dai yanzu kungiyar Chelsea ta kusa kammala cinikin takwaransa na Jamus, Timo Werner, wanda yake buga wasa a kungiyar RB Leipzig, hakan yasa ake ganin yanzu Manchester United da Bayern Munchen ne kadai za su fafata a kan dan wasa Havertz.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: