Dole Iyaye Su Kara Sa Ido Kan Ilimin Yaransu -Farfesa Victor

Iyaye

Wani daga cikin masu kishin ci gaban harkokin ilimi na rayuwar al’umma, Farfesa Victor Ibrahim La’ah ya bukaci masu ruwa da tsaki a Arewacin Nijeriya da kungiyoyin ci gaban al’umma da su hada hannu wuri guda domin ganin an inganta rayuwa tare da samar da ilimi mai inganci da hanyoyin ayyukan yi ga matasa maza da mata.

 

Ambasada Victor Ibrahim ya bayyana haka be alokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce babu wata nasara ko ci gaba da jama’a za su samu ba tare da hadin kai da kaunar juna da kuma ingantacce ilimi da sana’oin dogaro da kai ba. Farfesa Victor Ibrahim ya ci gaba da cewa, gwamnatoci na yin bakin kokarinsu, don haka ya zama wajibi ga iyaye su ci gaba da sanya idanu a kan harkokin karatun yaransu. Haka kuma ya ya yi kira ga kungiyoyin ci gaban al’umma da su taimaka wajen shirya tarukan kara wa juna sani da wayar da kan matasa domin fahimtar mahimmancin neman ilimi mai nagarta da sana’oin dogaro da kai.

 

Hakazalika Farfesa Ibrahim mai nasara ya yi amfani da wannan dama inda yayi kira ga daukacin al’umma cewa, tallafawa rayuwar yara marayu da mabukata dake cikin al’umma hakki da ya rataya a wuyan kowa da kowa, son haka sai ya bukaci jama’a  dasu ci gaba da yin addu’o’in dorawar zaman lafiya da hadin kan  al’umnar kasar nan.

Exit mobile version