Daga Abubakar Abba
Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya zuwa yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai bashi kunya ba a kan harkokin tafiyar da mulkin kasar nan.
A hirar sa da Gidan Talabijin na CNN ya ce, “Buhari bai zai iya kawo canji ba a cikin dare guda, dole ne a sara ma sa a kan nasarorin da ya samar a cikin shekaru biyun sa da darewa a kan
karagar mulki”.
Da yake tsokaci a kan kalubalen da kasashen Afirka suke fuskanta kuwa, Obasanji ya yi nuni da cewa “akwai matsalar ta yaya za mu iya ciyar da al’ummar mu da suke kara yawa? Ya za mu samar ma su da aikin yi? Harkar ba za ta ci gaba da kasancewar komai zan-zan ba”.
Ya kara da cewa ba yadda za ai a ce, “mu zauna kawai muna cikin daular jin dadi kamar zamanin da ya wuce a baya sannan muna mafarkin za mu kawo wani canji, tabbasa sai an canja yanayin da muke ciki na rashin samun cigaba da sunan jin dadi, kuma canji ya riga ya zo yanzu.”