Connect with us

WASANNI

Dole Mu Dage A Wasan Mu Na Athletico Bilbao

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Barcelona, Ernesto Balberde ya bayyana cewa, rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a hannun kungiyar Legannes a gasar Laliga shammatar su ta , kuma ya kamata su dage su samu nasara a wasansu na gaba da Bilbao.

A karon farko Barcelona ta yi rashin nasara a hannun kungiyar da gaba daya bata ci wasa ba a kakar wasan wannan shekarar halin da ya sa Barcelona ta yi rashin nasara ta farko kenan a kakar wasan wannan shekarar.

Dan wasa Philliph Coutinho ne ya cillawa Barcelona kwallonta ta farko a cikin minti na 12 da fara wasan, sai dai daga baya kungiyar Legannes ta farke kwallonta ta hannun Nebil El Zhar da kuma Oscer Rodriguez, wanda ya kara kwallo ta biyu yayin da Barcelona ta kasa farkewa ita kuma.

“Wannan wasan ya shammace mu, domin babu wanda ya taba zaton za mu yi rashin nasara a hannun kungiyar Legannes, amma kuma ba ina raina kungiyar ba ne, kawai dai ina duba yadda ‘yan wasanmu ba su taba tunanin za su samu matsala ba ne,” in ji Balberde.

Ya ci gaba da cewa, “Nan gaba muna da wasa da tsohuwar kungiya ta Athletico Bilbao, kuma mun san irin yadda suke buga kwallo, hakan yana nufin sai mun sake dagewa da mayar da hankali akan kowanne wasa idan har muna son kai wa ga nasara”

Shi ma dan wasan baya na kungiyar Sergi Roberto, ya bayyana cewa da farko sun raina Legannes sai da suka ga sun saka musu kwallaye biyu sannan kuma lokaci ya fara tafiya sannan suka farka, amma yanzu sun dauki darasi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: