Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Dole Mu Rage Dogaro Da Danyen Mai Wajen Samun Kudaden Shiga – Emefiele

by Yusuf Shuaibu
December 7, 2020
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Emefiele
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefiele ya bayyana cewa, akwai bukatar kasar nan ta rage yawan dogaro da danyan mai wajen samun kudaden shiga, domin samun dai-daita canjin kudaden ketare. Emefiele ya bayyana hakan ne a garin Abuja, wajen taron bayan da kyaututtuka na gasar kwallon gora na karshen shekarar 2020, wanda CBN ta gudanar. Mataimakin gwamna a bangaren haduwar ayyuka, Mista Edward Adamu shi ya wakilci gwamnan Babban Bankin. Ya bukaci kasar nan da ta dauki matakan bunkasa sauran fannonin tattalin arziki domin farfadowa daga matsin tattalin arziki.

A cewarsa, wannan ya zama wajibi domin fita daga matsin tattalin arziki da kasar nan ta fada. Ya kara da cewa, ba za a bar wasanni a baya ba wajen tabbatar da bunkasa kasar nan tun da dai ana fuskantar matsaloli a kasuwar canjin kudade, inda dala take kara hauhawa. Ya ce, yana shirya wasanni masu yawa a cikin kasar nan ciki har da kwallon gora. Ya jaddada cewa, Babban Bankin Nijeriya ba zai taba durkusar da kokarin matasa ba, saboda matasa da yawa suna samun kudade a harkokin wasanni a kasashen ketare.

samndaads

“A shirye Babban Bankin Nijeriya yake wajen bunkasa wasan kwallon gora domin inganta matasa maza da mata da ke cikin kasar nan.

“An dai shirya wannan wasan ne domin ci gaba da martaba Nijeriya a idon duniya ta bangaren harkokin wasanni

A cewarsa, ta hanyar bunkasa sauran fannin tattalin arziki, Babban Bankin Nijeriya zai sami damar gabatar da manufofi wadanda za su samar da aayyukan yi a cikin kasar nan.

“CBN ya dade yana samarwa masa sana’o’i ba ma a bangaren wasanni ba har ma a bangaren samar da shirin kudade wanda ke sa matasa suna dogaro da kansu

“Wannan ya hada da shirin samar wa matasa sana’o’I da shirin bunkasa kananan sana’o’I da samar da cibiyoyin karkira.

“Sauran sun hada da shirin bunkasa noma da bangarorin kamfanoni masu zaman kansu.”

A cewar Emefiele, CBN ya samar da shirin tallafa wa manoma domin bunkasa harkokin noma ta yadda za a samar da mabambamtan amfanin gona kamar irin su shinkafa da sauran amfanin gona guda tara. Ya bayyana cewa, shirin ya yi matukar tasiri wajen rage yawan shinkafar da ake shigowa da ita daga kasashen ketare, yayin da aka bai wa manoma bashi domin su samar da ishasshen abinci a cikin kasar nan. Ya ci gaba da cewa, ana kira ga ‘yan Nijeriya da su yi kokarin amfana da wannan shiri wajen ci gaban kasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, CBN ya shirya wannan gasar kwallon gora ne a tsakanin ma’aikatansa wanda ake gudanarwa a duk kasarshen shekara.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ma’aikatan INEC Biyu Sun Yi Batan Dabo A Zaben Dan Majalisar Zamfara

Next Post

Hukumar FIRS Ta Tattara Harajin Naira Tiriliyan 4.17 Daga Janairu Zuwa Oktoba

RelatedPosts

Matatun

Matatun Man Nijeriya Sun Lakumi Biliyan 152.08 Ba Tare Da Tace Digon Mai Ba

by Yusuf Shuaibu
18 hours ago
0

A cikin sabon rahoton kamfanin main a kasa (NNPC) ya...

Layin Dogo

Gwamnati Za Ta Kashe Biliyan N71 Wajen Kwangilar Titinan Dogo Shida

by Yusuf Shuaibu
2 days ago
0

Gwamnatin tarayya za ta kashe kudade wajen gudanar da hanyoyin...

TAJBank

TAJBank Na Kokarin Inganta Harkokin Ilimi A Nijeriya

by Yusuf Shuaibu
2 days ago
0

Bankin TAJBank wanda yake gudanar da kasuwancinsa ta tare da...

Next Post
Hukumar FIRS

Hukumar FIRS Ta Tattara Harajin Naira Tiriliyan 4.17 Daga Janairu Zuwa Oktoba

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version