Abubakar Abba" />

Dole Ne Gwamnatin Tarayya Ta Bankado Masu Daukar Nauyin Zanga-Zangar EndSARS, Cewar Gamayyar Kungiyoyi

Nauyin Zanga-Zangar EndSARS,

Gamayyar kungiyoyin farar hula 200 sun yi tir da barnar da masu zanga-zangar a rusa jami’an ’yan sanda na SARS suka yi a wasu ofisoshin ‘yan sanda, cibiyoyin Gwamnati, kone wasu gine-ginen gwamnati da kuma wawushe dakin adana makamai a jihar Legas Ogun, Aba Nnew da kuma a wasu sauran sassan da ke a Kudu.

A cewar kungiyoyin, hakan ya nuna a zahiri cewa, masu aikta mugayen laifula a kasar nan, sun fake da masu zanga-zangar domin cimma wata wata bakar manufarsu na karya lagon jami’an tsaron kasar nan karfin da yaji.

Sukar tasu ta na kunshe a cikin sanawar da Dakta Banjo Ayodele na kungiyar kare yancin yan adam (COHURA) da uwargida Ngozi Okocha data fito daga kungiyar (COAMOF) da uwargida Dakata Zainab Alkali data fito daga kungiyar (JUEGN) sai kuma Barista Festus Igbokwe, da ya fito daga kungiyar (JUPENE) suka rattabawa hannu suka kuma baiwa LEADERSHIP A Yau a Kaduna.

A don haka, kungiyoyin sun kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da a cikin gaggawa, ya umarci jami’an tsaro da su maido da doka da oda cikin hanzari, tare da bayyana fargabar cewa, idan akayi jinkiri wajen daukar matakai, hakan na iya kai kasar nan cikin halin ha’ula’i.

Sun kuma bukaci gwamnoni da su hanzarta fara gudanar da taro da matasan da ke a jihohin su kan zaman lafiya a jihohinsu.

“Mu na son yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta maido da doka da oda a Nijeriya, mu na kuma kira ga dukkanin gwamnoni da su fara taro da matasan da ke a jihohinsu domin hadin kan matasa shi ne hanya mafi dacewa ta samun zaman lafiya.”

Kungiyar sun kuma yi nuni da cewa, matasa da ke konawa da sata, ba masu zanga-zanga ba ne kamar yadda suka yi ikirari amma masu aikata laifi, ta nace cewa, inda suka kara da cewa, “Shugaba Muhammadu Buhari da jami’an tsaro, ya kamata su maido da doka da oda kafin kasar ta shiga wani hali.

“Da gaske mu ke mu na nuna bacin ranmu game da babban matakin rashin bin doka da aikata laifuka da ke faruwa a kasar a yau wanda wasu bata gari da daukar nauyin matasa da ‘yan daba ke aiwatar da su da sunan fidda fushinsu ga gwamnati.

“Wannan kashe-kashen, fashi, kone-klkone da lalata kadarori masu zaman kansu da na gwamnati da wadannan ‘yan daba ke yi a fadin kasar nan, ba abin da za a yarda da shi ba daga wajen gida da waje, kuma ya kamata kowa ya yi Allah wadai da shi.”

A cewarsu, “Don haka muna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da jami’an tsaro da su magance matsalar a cikin gaggawa, don maido da doka da oda.

“Mutane da yawa sun rasa rayukansu kamar yadda yawancin hanyoyin samun ababen more rayuwa suka lalata ta hanyar wadannan rukunin masu aikata muggan laifuka! Jami’an tsaro, inda sukayi nuni da cewa, asaboda hakan, yanzu ba sa iya komai saboda ba sa son a gan su suna amfani da karfi fiye da kima kan masu aikata laifin.”

Kungiyin sun yi nuni da cewa, “A yayin da lamarin ke ci gaba da tabarbarewa a kowane lokaci, mun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a dauki matakin da ya dace kafin a tsunduma mu cikin mummunan rikici.

“Dole ne a dakatar da wadannan masu laifi da masu daukar nauyinsu, a kamasu tare da kwato dukkan kayayyakin da suka sata tare da fuskantar hukunci.”

A cewarsu, kona ofisoshin ‘yan sanda da gangan tare da wawushe wuraren ajiya makamai a Lagas, Ogun, Aba, Nnewi da wasu sassa na Kudu, ya bayyana karara cewa, wadannan mutane manyan masu laifi ne wadanda ke neman hanyoyin da za su raunana hukumomin tsaron kasar nan.

“Mu na kira ga jami’an tsaro da kuma matasan mu da ke da kyakkyawar niyya su tashi su kare kasar a yanzu.

“Wannan ya nuna karara cewa, wadannan matasa ana daukar nauyinsu ne kuma sun fito ne ba wai dan kansu ba, saboda haka, muna kira ga dukkan matasan Nijeriya da su tashi tsaye wajen kare kimarsu daga masu son yin amfani da damar da zanga-zangar don kawai su cimma bukatunsu na son rai.

“Duk da cewa muna maraba da da hadin kai da kai na kasa da kasa, amma muna umartar su da su yi bincike mai kyau kafin su shiga cikin lamuran kasar mu, amma duk wani abu sabain hakan, wannan za a dauke shi a matsayin kokarin harzuka matasa don yin tunzuri ga gwamnanti.

“Babu wata kasa a duniya da za ta lamunci lalata abubuwa kamar yadda aka gani a‘ yan kwanakin nan, masu gudanar da zanga-zangar a Nijeriya sukayi ba, ba tare da daukar matakan dawo da doka da oda ba, inda suka kara da cewa, “Nijeriya tamu ce kuma kasa ce mai cikakken iko wacce ke da dukkan dokoki.”

Exit mobile version