Khalid Idris Doya" />

Dole Ne Kowanne Lauya Ya Yi Shigar Da Ta Dace A Gaban Kotu Ko Mu Ki Saurarensa -CJ

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Babban mai shari’a a babban birnin tarayya Abuja, Justice Ishak Bello ya gargadi kowani Lauyan da ya sake halartar zaman kotun FCT ba tare da yin shigar da ta dace da shigar lauyoyi ba, kotun za ta yi facakali da saurarensa ta kuma ki kula shi.

Justice Bello ya bayar da gargadin ne a cikin wata sanarwar da ya fitar dauke da sanya hanun babban sakataren babban kotun FCT, Babangida Hassan.

Sanar ta ce “A bisa kokarin da Mai shari’a Ishak Bello ke yi na ganin ya tabbatar da rage yawaitar rashin yin shigar da ta dace daga lauyoyin da suke bayyana don yin shari’a a gaban kotu ne ya sanya ya bijiro da cewar dole suke shigarsu da ta dace da doka”, In ji Shi.

Ya kara da cewa, doka ta 6(b) da ke cikin ka’idojin kwarewar dabi’ar a cikin sha’anin shari’a ta 2007 ta na cewa ne “a lokacin da kotu ke zamanta, lauya ba zai nuna matsayinsa ko ya bayyana kansa ba, ba tare da amincewar mai shari’a ba, zan iya ciresa a sakamakon shiga kotu ba da kayan da ta dace ba. dole ne lauya ya kasance a kowace lokaci yana shiga ta kama da mutunci domin ya nuna halayyar kwarai tun daga kan tufafinsa ne, ko kuma irin adon da zai cancada wanda ka iya sanya ya jawo hankali ya dawo kan shi,”

Ya ce, ka’idar take cikin shigar da aka tsara wa lauya na miji ita ce shiga bakar kaya riga fari, farin littafi, bakin safar kafa, bakin takalmi, bakin wando da ake tsammaninsa da sawa a kowani lokaci idan zai shiga gaban shari’a.

Ga mata kuwa, an ce suna iya sanya riga mai dan launin baki-baki, siket shi ma mai launin baki-baki, wajibi ne ta rufe jikinta har gwiwowinta, sannan za ta sanya bakar takalmi, farin abun rubutu da kuma su yi adonsu matsakaici.

Sanarwar ta ce ya wajaba a kan kowani lauya yake sanyawa gami da yin irin wadannan shigar a kowani lokacin da lauya zai kasance a gaban kotu.

“Kowani lauya kula ya kuma dauki wannan da muhimmanci, dukkanin lauyar da ya fatali ko ya ki amsar wannan tsarin to ba za a sauraresa ko shaidunsu a gaban babban kotun FCT ba,” A cewar Sana’arwar.

A jiya Talata ne Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya rantsar da mai shari’a Yakubu Gyang Dakwak a matsayin cikakken babban Alkalin Alkalai na jihar Filato.

Dakwak wanda ya kasance mai rikon mukamin babban Alkalin tun a watan Satumban 2017 biyo bayan da tsohon Alkalin-Alkalai na jihar Justice Pius Damulak ya yi ritaya daga aikinsa gwamnati.

A cikin jawabinsa a wajen rantsar da sabon Alkalin-Alkalai, Gwamnan Lalong, ya bukaci sabon CJ din da ya yi amfani da dukkanin damar da ya samu wajen kokarin rage karfin cin hanci da rashawa da suka addaba kasar nan.

“Fannin shari’a wani fanni ne da ke da karfin ikon yin mai iyuwa wajen daidaita al’umma da su dawo kan bin doka da oda. Don haka, ina kiranka a bisa wannan mukamin da ka samu ka yi amfani da damarka wajen kawo gyara a cikin al’umman Nijeriya kan rashin bin doka,” In ji Gwamnan.

Gwamnan Jos din ya kuma ce kalubalen da ke gaban sabon CJ din sun hada da kokarin kawo kan rashin da’a, aiyukan cin hanci da rashawa da sauransu, ya bukace sa da ya yi aikinsa bisa gaskiya.

A jawabinsa na godiya, babban Alkalin Yakubu Gyang Dakwak,  ya gode kwarai a bisa amince masa da gwamnan ya yi na bashi wannan mukamin yana mai daukan alkawarin gudanar da aikinsa cikin gaskiya da adalci da kuma kokarin shawo kan matsalolin da suke jibge.

 

 

Exit mobile version