Connect with us

WASANNI

Dole Sai Mun Dage Sosai A Wasanmu Da Rasha, Cewar Sergio Ramos

Published

on

Kyaftin din tawagar yan wasan kasar Sipaniya, Sergio Ramos, ya bayyana cewa duk da cewa kasar ta Sipaniya ta samu tikitin zuwa zagaye na gaba na gasar cin kofin duniya amma kuma har yanzu akwai gyara musamman yadda suke gudanar da wasa a bangare yan wasan baya.
Ramos ya bayyana hakane bayan an tashi daga wasan da kasar ta Sipaniya ta buga 2-2 da kasar Morocco a gasar a ranar Litinin wanda sakamakon wasan yasa suka samu wucewa zuwa zagaye na gaba yayinda kasar Portugal take a matsayi na biyu sai kuma kasashen Iran da Morocco wadanda duk sun fice daga gasar.
“Dole sai mun canja yadda muke buga wasa saboda akwai gyare-gyare dayawa muna buga wasa amma kuma ba kamar yadda yakamata ace muna bugawa ba saboda haka akwai bukatar mu sake nutsuwa domin nemo inda matsalar take” in ji Ramos
Yaci gaba da cewa “muna da yan wasan gaba masu taimakawa sosai kuma suna zura kwallaye a raga amma kuma a bangaren baya bama kokari kuma yakamata mu gane cewa daga yanzu idan mukayi kuskure aka zura mana kwallo a raga kuma aka tashi a haka mun fice daga gasar kenan”
Kasar Sipaniya dai bata fito daga cikin rukuni ba a shekara ta 2014 a gasar da aka buga a kasar Brazil kuma duk da cewa a shekarar itace take kare kambu domin itace ta lashe gasar a shekara ta 2010 wanda aka buga a kasar Africa ta kudu.
Kasar Sipaniya dai zata fafata da kasar Rasha mai masaukin baki a gasar a wasan zagaye na biyu da zasu fafata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: