Connect with us

WASANNI

Dole Sai Mun Rage Yin Kuskure A Wasannin Mu

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa dole sai ‘yan wasan kungiyar sun rage yin kura kurai idan har suna son samun nasara a wasanninsu na gaba.
United dai tasamu nasara a wasan farko data buga da kungiyar Leceister City sai dai tasha kashi a hannun kungiyar Brighton Albion a wasa na biyu na firimiya da suka fafata a ranar Lahadin data gabata daci 3-2.
Sai dai Mourinho ya bayyana cewa idan har kungiyar tanason samun nasara a wannan shekarar dole sai ‘yan wasa sun rage yin kuskure saboda yawan yin kuskure shine yake sawa kungiya tayi rashin nasara a wasa.
“Wasan farko da muka buga bamuyi kuskure da yawa ba kuma mun samu nasara akan Leceister City amma a wasanmu na biyu da mukayi kuskure da yawa munyi rashin nasara kuma daman haka abu yake yawan yin kuskure shine yake kawo rashin nasara” in ji Mourinho
Yaci gaba da cewa “ Duk kungiyar da tafiya yin kuskure a wasa dole sai tasamu matsala saboda sakamakon kuskure a wasa shine rashin nasara kuma munyi a wasanmu da Brighton a satin daya gabata”
A yau ne dai manchester United za ta fafata wasa na uku da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a wasa na uku na gasar Firimiya a filin wasa na Old Trafford da misalin karfe takwas na dare.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: