Abba Ibrahim Wada" />

Dole Sai ‘Yan Wasana Sun Sake Dagewa, Cewar Kociyan Manchester

A karon farko cikin shekaru 30, Manchester United ta fara kakar wasanni mafi muni bayan ta samu maki tara daga cikin wasanni bakwai da ta buga a gasar Firimiyar Ingila, inda Liverpool mai jan ragamar teburin ta ba ta tazarar maki 12.

Kungiyar ta yi fatan samun nasara a karan-battar da ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal  a filin wasa na  Old Trafford, amma suka tashi kunnen doki 1-1 duk da cewa Manchester United din ta samu damar maki daban-daban.

Pierre Emerick Aubameyang na Arsenal ne ya haramta wa Manchester United samun nasara a karawar, inda ya jefa mata kwallo a raga a minti na 58, abin da ya soke kwallon da Manchester ta fara zurawa a minti na 45 ta hannun Scott Mc Tominay.

Da farko, an soke kwallon da Aubameyang ya zura saboda zaton cewa, ya yi satar fage, amma daga bisani, na’urar taimaka wa alkalin wasa, ta tabbatar da ingancin kwallon bayan da aka tabbatarwa da alkalin wasa ciwa kwallon bata da matsala.

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce, akwai bukatar ‘yan wasansa su kara kaimi wajen samun nasara a wasanninsu, musamman ganin yadda ba sa iya zura kwallo fiye da guda a ragar abokan hamayyarsu a sabuwar kakar.

Kuma Solkjaer ya bayyana cewa shine wanda ya dace ya cigaba da koyar da kungiyar duk da cewa yana fuskantar kalubale da suka daga bangarori da daman a ciki da wajen kasar Ingila saboda rashin kokari sai dai yace nan gaba kadan komai zaiyi daidai.

Exit mobile version