Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Dole A Saka Na Hannun Daman Buhari A Sunayen Ɓarayin Gwamnati

by Tayo Adelaja
October 22, 2017
in RAHOTANNI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa, dole ne a sanya har na hannun daman Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a jerin sunayen da gwamnatin tarayya za ta saki na ɓarayin gwamnati, ya na mai yabawa da wannan mataki da gwamnati ke shirin ɗauka na yin terere.

samndaads

A ta bakinsa ya yi habaicin cewa, “ba ’yan lema kaɗai ya dace a saka a jerin sunayen ba, har ma da ’yan tsintsiya da kuma na hannun fadar shugaban ƙasa.”

Sanata Sani, wanda ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Facebook, ya ce, hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na bayyana sunayen abin a yaba ne. Don haka ya na fatan ba za a taƙaice shi a kan ’yan bora kurum ba, za a haɗa da dukkan ’yan mowa masu kashi a gindi

Ministan shari’a kuma antoni janar na tarayya, Alhaji Abubakar Malami, SAN, ne ya bayyana hakan a wani taro da ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta gudanar a cikin makon nan, inda ya yi ƙarin haske da cewa, matakin ya biyo bayan hukuncin da kotu tarayya da ke Lagos ta yanke ne, wanda ta umarci gwamnatin tarayya da ta buga jerin sunayen ɓarayin da kuma yawan adadin kuɗin da a ka amso daga hannunsu.

Irin waɗannan kalamai na Sanata Sani ba su ne na farko ba da su ka taɓa jagwalo abin cece-kuce, inda ko a kwanakin baya an ruwaito matar shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ta na yin shaguɓe kan wata magana da ya furta.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Za Mu Tantance ’Yan Gandujiyya Da ’Yan Kan Katanga – Iliyasu Kwankwaso

Next Post

BABBA DA JAKA

RelatedPosts

Neja

Tsaro; Sakataren Gwamnatin Neja Ya Nemi ‘Yan Bindiga Su Aje Makamai

by Muhammad
5 days ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, Sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane...

Tinubu

Sanata Tinubu Ya Bukaci A Kara Samar Da Zaman Lafiya Tsakanin Al’umma

by Muhammad
5 days ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Jagoran jam'iyyar babbar jam’iyya mai mulkin...

Miyagun Kwayoyi

Shugaban NDLEA Ya Yi Alkawarin Fattatakar Dillalan Miyagun Kwaya A Nijeriya

by Muhammad
5 days ago
0

Daga Bello Hamza, Shugaban hukumar NDLEA, Brig. Gen. Buba Marwa...

Next Post

BABBA DA JAKA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version