Connect with us

Madubin Rayuwa

Domin Iyaye: Hanyoyi 20 Na Rigakafin Yi Wa Yara Fyade

Published

on

Salamu alaikum warahmatullah. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon cikin shafinku mai farin jini na zaman tare.

A wancan makon da ya gabata mun yi stokaci akan illar rabuwar aure wanda yake daya daga cikin kofofine dasuke bama mutanen nan masu mummunar akida ta lalata yara mata awannan zamanin domin mafi yawan koke koken damuke samu idan muka bincika mukan samu yaran basu tare da uwarsu ko babu uban sabida raunin kulawa dasukan sama yakanbawa irin wayyannan mutane kafa ta lalata rayuwar wayannan yara. Don haka a wannan makonma za mu daura daga inda muka tsaya tare da janyo hankalin iyaye da shuwagabannin makarantu,al’ummar unguwa,shuwagabannin al’umma da hukumomin akan mutashi tsaye domin kawar da wannan mummunar dabi’a da ke barazana ga yaranmu domin irin wadannan mutane suna ko ina, lungu da sako, birni da kauye kuma ba su da kama domin ta kaiga an kawo mana wani rahoto a kan uban da yake lalata da yarinyarsa yar shekara tara, toh kun ga a nan babu wani tabbas da muke da shi akan kowaye. Sau da yawa sakaci ko ganganci ke sa hakan ya faru, wani kuma kaddara ce kawai daga Allah wacce ba ta da makawa.

Misali, an kawo mana wani labari a kan yadda wata mace ta dauko yaron kanwarta dasunan bai da lafiya ta yi masa magani sa’annan ta hada shi daki daya su rika kwana da yarinyarta a inda aka fahimci yarinyar na da ciki. Da aka tuhumi yarinyar sai aka samu cewa wannan yaro dai da ake ganin shi mara lafiya shi ya yi wa yarinyar nan cikin. To kun ga wannan lamari akwai ganganci cikinsa.

Sau da yawa mukan aikata ganganci ko halin ko inkula a kan yaranmu, sai idan abu ya faru mu ce kaddara ko an cuce mu inda mu muka fara cutar kanmu.

Misalin irin abubuwan da ya kamata mu iyaye mu yi wajen kula domin kiyaye yaranmu daga sharrin wadannan mutane masu fyade su ne kamar haka.

1. Mu yi kokarin cusa tarbiyya da kyawawan dabi’u ga yaranmu da nunashesu halas da haram.

2. Mu kasance masu yawan yiwa yaranmu addu’a ta neman tsari daga kowane irin sharri.

3. Mu kasance masu kyakyawar kalma gare su koda sun bata mana rai ne domin shi ne zai taimaka wa tarbiyya domin da yawa iyaye kan jawo wa yaransu sharri da bakinsu.

4. Mu zama masu sa ido ga sha’anin yaranmu shige da ficensu da irin kawayen da suke mu’amula da su da yawan sauraren irin hirarsu amakaranta da ta kawayensu hakika zaitemaka mana wajen fahimtar kowane lamari da irin dabi,ar kowace kawa.

5. Mu kasance muna yawan duba jakar makarantarsu ba tare da sun sani ba tare da sa ido akan wasu abubuwa sababbi da yake cikin jakarsu ko za su shigo da shi gida.

6. Mu yawaita jan hankulansu a kan kiyaye karbar wani abu daga wani ko wata, sannan mu kiyaye wajen kokarin basu wani abu da za su tafi makaranta dashi kamar sweet, biscuit daidai karfinmu inda koda sun ga na wani ko wata ko an ja hankalinsu da shi bazai burge su ba.

7. Mu yi kokarin kasancewa da yaranmu duk rintsi duk wahala domin tarbiyyarsu ta inganta domin uwa da uba su suka fi cancanta da bawa yaransu tarbiyya, saidai kaddara irin ta mutuwa.

8. Mu yawaita kai ziyara lokaci lokaci ga yaranmu yayin da suke makaranta.

9. Mu dinga kiyaye irin fina-finai da za mu dinga barin yaranmu suna kallo.

10. Mu nun awa yaranmu susan kowane bangare na jikinsu tare da hikima wajen ilmantar da su da tsoratar da su akan wasu bangarori na jikinsu da ba a tabawa.

 

11. Mu kasance masu sakewa da yaranmu wajen hira da yi masu wasu tambayoyi domin su ma su sake da mu don su samu damar sanar da mu wasu abubuwa idan sun faru gare su.

12. Mu dinga ba makwabtanmu ko abokanmu dama ko fuska inda za su sanar damu abin da yaranmu ke ciki awaje.

13. Mu yawaita jan kunensu da gaya masu kada wani ya kirasu su je sannan kada wani ya basu abu su karba. Mukasance masu yawan kula dabi’unsu da kiyaye canjin yanayi a tare da su.

14. Jaka mu kiyayi dora wa yaranmu tallace-tallace domin kowa zai iya kiran yarinya a ko ina da sunan zai sayi kayan sayarwarta, kuma ba ni ganin talla zai maganin talauci idan dole da bukatar hakan ina ba mu iyaye shawarar mu fita tallan da kanmu ya fi mana kwanciyar hankali a kan mu tura yaranmu.

15. Mu kiyayi kai su gidan wanke-wanke ko saida abinci domin muna yawan samun labari kan lalacewar yara a sanadiyyar tallace-tallace ko aiki wajen sayar da abinci.

16. Mu yawaita nasiha da fadakarwa ga yaranmu akan yadda rayuwa take da nuna masu me kyau da Mara kyau da illarsa da alkhairinsa

17. Haka ya kamata shuwagabannin makarantu su kula da alakar yara da Malamai domin lokacin makaranta kulawa da amanar yaran nan na hannun Hukumar makaranta.

18. Haka shuwagabannin al’umma da mazauna unguwa suna da hakki a kan kulawa da sa ido akan shige da ficen mutanen unguwar, yin haka zai matukar taimaka wajen tsoratar da irin wadannan mutane.

19. Kafa kungiyoyi na wayar wa da mutane kai da tsayuwa domin kawarda cin zarrafin yara mata da maza har da manya kamar irinsu ‘Help For The Bictims Of Matrimonial Abuse Foundation’ a kan cutar da yara mata/maza

20. Haka hukuma tana da muhimmiyar rawar da za ta taka tawajen kawarwa/rage yawaita lalata yara kanana tawaje tsayuwa kan hukumcin daya dace akan laifin fyade ko lalata yara.

 Hakika idan mun kiyaye Allah zai kiyaye mana, duk dacewa ba mu da hikima ba mu da dabara. Amman hakika addu’a da kokarinmu su zasu taimaka mana da yardar Allah domin hakkinmu ne mu kula da tarbiyya da abin da zai cutar da yaranmu, domin tabbas Ubangiji Allah kamar yau ne zai tambaye mu akan kiwon da ya bamu. Allah ya shirya mana tare da kawo karshen wannan irin masifu, amin summa amin.

Sai mun hadu mako mai zuwa cikin yardar Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: