Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Don Me ’Yan Siyarar Amurka Ke Iyakacin Kokarin Dakile Kafofin Yada Labarai Cikin Gida?

Published

on

Wata kafar yada labarai ta Amurka ta ba da labarin cewa, wata takardar cibiyar kandagarkin cututtuka ta Amurka CDC ta fito fili, inda ta ruwaito bayanin Twitter da fadar White House ta bayar, wanda ke cewa gidan rediyon Amurka na VOA na tallafawa kasar Sin, kuma fadar ta nemi hukuma mai kula da harkokin yada labarai ta CDC da ta ki yarda da zantawar da VOA ke yi da manema labarai. Daga baya kuma, shugaban VOA da mataimakinsa, sun sanar da sauka daga mukaminsu, kuma sun ce, shugabansu na da ikon sanya wasu su maye gurbinsu.

An ce wannan shi ne matakin da gwamnatin Amurka ke dauka don mayar da martani ga VOA, bayan a Afrilu ta zarge ta da cewa, tana gefen kasar Sin.
’Yan siyasar Amurka suna yunkurin dora laifi kan kasar Sin, saboda sun gaza daukar matakai da suka dace don magance cutar COVID-19, har su dakile kafofin yada labarai cikin gida. Duk wata kafa dake ba da labari bisa gaskiya game da yadda Sin take yakar cutar, shugabannin Amurka za su kai hari kan ta.
Ban da wannan kuma, ’yan siyasar Amurka suna yunkurin ba da umurni a siyasance, don kayyade abubuwan da za a gabatar a kan shafin Intanet na sada zumunta, don su mayar da wadannan kafofin yada labarai a matsayin wani mataki na cimma burinsu na siyasance. Kwanan baya, Twitter ta sanar da cire masu amfani da Twitter fiye da dubu 170, da zar wai suna da alaka da gwamnatin kasar Sin, suna kuma yayata maganar dake dacewa da moriyar kasar Sin kan ra’ayin siyasa bisa yanayin wurin.
A halin yanzu, duk duniya ta san dalilin da ya sa wasu ’yan siyasar Amurka suke daukar wadannan matakai, wato suna yin fuska biyu kan ’yancin fadin albarkacin baki, da Demokuradiyya da kuma hakkin Bil Adama, duk wadannan abubuwa matakai ne na cimma burinsu, idan ba su bukata sai su yi watsi da su. (Mai Fassarawa: Amina Xu)




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: