Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home KASASHEN WAJE

Donald Trump Na Da Tabin Hankali, In Ji Kim Jong-Un

by Tayo Adelaja
September 23, 2017
in KASASHEN WAJE
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A ci gaba da musayar zafafan kalamai tsakanin kasar Amurka da Koriya Ta Arewa, Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mutum mai tabin hankali.

Kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa da ke birnin Pyongyang ya ambato Kim Jong-un na cewa shugaban Amurka zai yaba wa aya zaki saboda jawabin da ya yi tun farkon wannan mako a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Donald Trump ya fada wa taron cewa idan tura ta kai Amurka bango, to za ta kare kanta, kuma sai ta yi raga-raga da Koriya Ta Arewa.

Trump din dai ya fadin bakar magana kan Kim Jong-un inda ya kira shi da sunan ‘Mai Roket”.

A ranar Alhamis ma, Donald Trump ya sanar da kakaba karin takunkumai a kan Koriya Ta Arewa, har ma ya yaba wa mahukuntan China.

“Ina mai matukar alfaharin fada maku, kamar yadda mai yiwuwa kuka ji dazun nan cewa babban bankin China ya sanar da sauran bankunan kasar cewa su daina hulda da Koriya Ta Arewa, to wannan abu ya yi dadi.” In ji Trump.

Donald Trump ya ce bankunan kasashen waje za su fuskanci zabi karara cewa ko dai su yi hulda da Amurka ko kuma su yi kasuwanci da gwamnati maras bin doka ta Koriya Ta Arewa.

Ya bayyana dokar shugaban kasa da ya sanya wa hannu a matsayin wani sabon abu mai karfi da ya ce za ta yi magani wata kasa guda, kuma ita ce Koriya Ta Arewa.

SendShareTweetShare
Previous Post

• Gwamna Aminu Waziri Tambuwal tare da Shugaban Ohaneze Ndi’gbo, John Nnia Nwodo a ziyarar da ya kai gidan gwamnatin jihar Sakkwato ranar Alhamis da ta gabata.

Next Post

Majalisar Dokokin Uganda Ta Jingine Batun Gyaran Kundin Tsarin Mulki

RelatedPosts

Mijin Sarauniya Elizabeth Ta Ingila Ya Mutu

Mijin Sarauniya Elizabeth Ta Ingila Ya Mutu

by Muhammad
3 days ago
0

Rahotanni daga Fadar Buckingham ta kasar Ingila sun tabbatar da...

Nijer

Matan Nijer Sun Dage Kan ‘Yancinsu Bayan Kotu Ta Sako Wasu Shugabanninsu

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun sako...

Magufuli

Muhimman Abubuwa Goma Game Da Tsohon Shugaban Tanzaniya John Magufuli

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Al'ummar kasar Tanzania suna zaman makokin...

Next Post

Majalisar Dokokin Uganda Ta Jingine Batun Gyaran Kundin Tsarin Mulki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version