Abba Ibrahim Wada" />

Dortmund Ta Dauki Sabon Mai Koyarwa

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta  Borussia Monchengladbach, Marco Rose ya sanar cewar zai koma jan ragamar abokiyar hamayya Borussia Dortmund a badi idan an kammala buga kakar wasa ta bana.

Gladbach ta ce Rose, mai shekara 44, ya amince zai bar kungiyar duk da saura kaka daya yarjejeniyarsa ta kare kuma tuni ya amince da duk yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund.
Dortmund wadda ba ta ce komai ba kawo yanzu tana neman wanda za ta bai wa aikin horar da ita, domin maye gurbin Lucien Fabre wanda kungiyar take tangal-tangal a hannunsa tun bayan karbar ragamar aiki.
“Inaso kafa tarihi kamar yadda manyan masu koyarwa a duniya suka kafa musamman a wannan kungiya ta Dortmund mai tarihi kuma ina fatan zan samu hadin kai daga wajen shugabannin kungiyar domin ci gaba” in ji Rose
Ya ci gaba da cewa “Zanyi kokarin ganin kungiyar da nake aiki da ita a halin yanzu ta lashe kofi  bana kuma kulla yarjejeniyar da nayi da Dortmund ba zata karkatar da kokarin da nakeyi ba na kammala kakar wasa da sakamako mai kyau”
An dade ana alakanta dan wasa Rose wanda aka haifa a birnin Leipzig da cewar shi ne zai maye gurbin Edin Terzic wanda ke aikin rikon kwarya a Dortmund sai dai daga baya bangarorin biyu basu amince da juna ba.
Rose ya fara jan ragamar kungiyar Gladbach daga Red Bull Salzburg a watan Yulin shekarar 2019, ya kuma kai kungiyar cikin ‘yan hudun farko a gasar Bundesliga a kakarsa ta farko sannan ya kuma kai kungiyar matakin zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League kuma a karon farko a tarihin kungiyar.
Bayan da ya ja ragamar wasanni 21 a bana, kungiyar tana ta bakwai a kan teburi da maki iri daya da na Dortmund wadda take ta shida da tazarar maki shida tsakaninsu da ta hudu a teburin na Bundes Liga.

Exit mobile version