Connect with us

Nahiyar Afirka

Dos Santos Zai Ajiye Shugabancin Jam’iyyar MPLA

Published

on

A yau asabar toshon shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos zai ajiye shugabancin jam’iyyar da ke kan karagar mulkin kasar MPLA, shekara daya bayan zaben da ya dora Joao Louranco a kan karagar mulki.
Mika ragamar jagorancin jam’iyar a hannun shugaba Louranco, na nufin kawo karshen shekaru 39 da tsohon shugaba dos Santos da kuma iyalansa suka share suna jan zarensu a kasar mai arzikin mai.
Hakazalika bikin mika jagorancin jam’iyyar da zai gudana a birnin Luanda, na zuwa ne a cikin wani yanayi na tsamin dangantaka tsakanin mutanen biyu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: