DPR Ta Kulle Gidajen Mai Shida A Anambara Tare Da Matsa Sayar Wa Akan Naira 145

Hukumar sanya ido akan yadda ake raba mai (DPR) ta kulle gidajen sayar da mai guda shida a jihar Anmbara sakamakon zargin boye man da sayar dashi sama da farashin da gwamnatin tΩaryya ta kayyade na naira 145 akan ko wacce lita.

Gidajen man da aka kulle suna a  yankin Awka da Onitsha da  Nkpor da kuma Obosi ne.

An ruwaito cewar man (PMS) ana sayar dashi tsakanin naira 220 zuwa naira 240 a kan lita daya a Awka da wasu sauran sassan jihar mallakar masu sayar  da mai.

Hukumar ta kuma jadda da farashin da gwamnatin tarayya ta kayyade na naira 145 akan ko wacce lita daya, inda ta rabar da man sama da lita sha shida kyauta ga ababen hawa.

Da yake jawabi ga manema labarai shugaban hukumar a jihar Mista Callistus Obodoechina yace za’a ci gaba da sanya ido har sai masu gidajen man sun bi ka’ida.

Obodoechina yace an rufe gidajen man ne saboda masu gidajen man suna sayar da mansu sama da farashin da gwamnatin tarayya ta kayyade da kin daidaita fanfunan su da zargin karkatar da man.

A bisa tsarin hukumar, ta yi wa ‘yan kasar nan alkawari wajen sayar masu da man, musamman PMS akan farashin da gwamnti ta kayyade.

Acewar sa, “ burin mu shine, don mu tabbatar da cewar dukan masu harkar man, suna sayar dashi a bisa farashin da gwamnti ta kayyade kuma ba tare da suna boye man ba ko karkatar dashi.”

Yace, “ a cikin kwana biyu, sun sanya ido akan sayar da mai sama da lita sha shida na PMS, inda ake sayar dashi akan naira 145 ga jama’a.

Obodoechina ya kara da cewa, “ mun kuma kulle gidajen mai shida da suka ki mayarda fanfunan su yadda suke, inda masu gidajen man suka fake da cewar kan fanfunan nasu suna da matsala.

Ya koka akan yadda masu sayar da man suke cutar masu sayen mansu, duk da matakin da gwamnati ta dauka akan lamarin.

Shima da yake nashi jawabin, wani jami’in hukumar Mista Uyinme Akpan,ya yi tir da yadda masu sayar da man suke yin kirin kudin man duk da sanya idon da hukumar keyi.

Akpan ya bayyana cewar duk gidajen man da suka yin hakan, zasu hadu da fishin hukuma, kuma hukumar zata ci gaba da sanya ido sanna kuma ya umarci alummar jihar dasu dinga kai rahoton gidajen mai da suke boye man.

A wata sabuwa kuwa, alummar jihar sun yabawa hukumar akan sanya idon da suke yi akan gidajen man.

Mista Chris Nduka  ya yi nuni da cewa, hukumar kadai dake jihar, bazata iya magance boye man da kuma karkatar dashi ba.

A karshe yace gwamnatin tarayya tana iya kokarinta ta hanyar hukumar don magance masu boye man da karkatar dashi.

 

Exit mobile version