Dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a qarqashin inuwar jam’iyyar APC, Dakta Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau) ya jaddada goyon bayansa ga sake zaven Shugaba Buhari a karo na biyu.
Dan takarar na gwamna ya yi wannan bayani na nuna goyon baya ne ga Jaridar LEADERSHIP A Yau, inda ya ce, har wayau suna nan tare da jam’iyyar APC.
Dan takarar na gwamnan ya kuma bayyana fatan da suke da shi na samun nasara don tabbatar da jam’iyyar APC ta yi takara a Zamfara a zabukan da za a gudanar a wannan shekara ta 2019.
Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne Hukumar INEC ta fidda jerin sunayen ‘yan takara na jihohi, inda a Jihohin Zamfara da Ribas babu ko mutum daya daga jam’iyyar gwamnati, wato APC. A dalilin haka ne mutane da dama ke bayyana takaicinsu da jimami na ganin jam’iyyar ba za ta yi takara ba musamman ma a Jihar Zamfara da kaso 90% na al’ummar wurin magoya bayan jam’iyyar ne.
Dr. Dauda ya yi wa magoya bayan jam’iyyar ta APc albashir da cewa, su kwantar da hankalinsu, jam’iyyar za ta tsayar da ‘yan takara a Jihar Zamfara, wanda bayanai za su fito cikin kwanaki kadan masu zuwa.