Connect with us

DAGA NA GABA

Dr. Uba Adamu: Gwarzonmu Na Mako

Published

on

Tunawa da Dr. Muhammad Uba Adamu (1935 – 2020)

Wannan waka Dr. Aliyu Akilu ya rubuta ta ne a 1975, ya yi ta ne, domin wani hangen nesa da ya ga Kantomman Kano na wancan lokaci, wato Dr. Uba Adamu. A hirar da na yi da Dr. Uba Adamu a gidansa cikin watan Afrilu, ya bayyana mi ni cewa “cikin 1974 ne su ka yi tunanin, kawo gyara a tsarin zamantakewar birnin Kano. A saboda haka su ka kawo wani tsari, wanda hakan ya haifar da gina manyan titina a Birnin Kano da yin kwalbatoci da kuma wajejen zuba shara. A wannan lokacin ne a ka yi manyan titinan da a ke amfani da su har yanzu a birnin Kano. A ka kuma yi mu su kwalbatoci a gefunansu da kuma wajejen zuba shara.”

A saboda jin dadin wannan aiki ne, ya sanya Dr. Aliyu Akilu ya yi wannan waka. Ga dai wakar mai taken ‘Gyaran Kano’ Daga Dr Aliyu Akilu 1975:

 

Zan je ziyarar shugaba

Dattijo Kantoma Uba.

 

Bazan shiru na kawai ta ba

In ba da na ce Rabbu ba.

 

Sarki guda daya wahidi

Bazan takaita kiransa ba.

 

Bayan fadar Allah da gai da

Manzo Muhammadu Mujtaba.

 

Me zai biyo bayan su ne

Na abin nufi da yake gaba.

 

Haka ne akwai wani dan batu

Da ba zan ki tunkarar sa ba.

 

Ga dai bayani dan kadan

A takaice ba dungunsa ba.

 

Niyar ziyara ce dani

Zancenta yau zan bayyana.

 

Mai tambaya ya so yaji

Domin ya amfana gaba.

 

Manufar ziyarar wacce nai

Maganarta tun farko gaba.

 

Ya zuwa ina wai zani kai

Mai tambaya bai aibu ba.

 

Zan bayyana masa ne ya ji

Bazan yi kwauro gun sa ba.

 

Zan dau ziyara ne ni kai

Ta kano gari ba kauye ba.

 

Wajen masoyina abin

kamna sahihin Shugaba.

 

Shine Muhammadu Adamu

Kantoma mai lakabi Uba.

 

Dattijo din nan adali

Mai tausayin jama’a Uba.

 

Bangon tama ki faduwa

Sha kabra garnakaki Uba.

 

Matsayinka din nan kai can

Canta da shi malam Uba.

 

Illimi zalaka ke gare

ka da kwarjini na kwarai Uba.

 

Ga hattara ga hankali

Kantoma ga hangen gaba.

 

Illimin makamar zamani

Da sanin sharia tun gaba.

 

Ka san su ka kuma dandake

Ba yau kawai ka tsire suba.

 

Birnin Kano da wajenta duk

Ta samu babban cigaba.

 

A wajen nizafa in ka du

Ba kauyuka ba a bar suba.

 

Balle cikin birnin fa

Ba wai bane ba inke ba.

 

Kwatami cakal yau babu shi

Shara butsa bamu ganta ba.

 

Sarari a hanya ya dadu

Albarkacin himmar Uba.

 

Duk tarkace an kauda su

Daga ko ina ba a bar shi ba.

 

Sababi da wane mun ka sami

wannan gimgimemen cigaba.

 

Mun samu kakkaifan mutum

Mai kokari ba kasa ba.

 

Gwarzon maza namijin tsaye

Inuwa ba a bisne ki ba.

 

Kantoma Muhammadu Adamu

Dattijo mai lakabi Uba.

 

Bompai da Rimin Dada sun

Maka godiya malam Uba.

 

Sabon gari da Tudun wada

Sun gode mai daraja Uba.

 

Tarauni su da Giginyu sun

Yi yabo ga mai daraja Uba.

 

Gandu Sharada da Dorayi

Da Salanta., Calawa gaba.

 

Jama’ar da ke Fanshekara

Duk sun yi san barka Uba.

 

Waika da Jajira, Gobira

Wa, sun yi godiya malam Uba.

 

Kurna, Fagged da Gwagwarwa

sun maka godiya malam Uba.

 

Na sauka Fanisau mutan

Gama sun game da yabon Uba.

 

Ungogo, Kunya suna fadar

Madalla-madalla Uba.

 

Wannan Sadauki adali

Dattijo bai yashe mu ba.

 

Kub! Dai yawa kuwa lara bugu

Daya ta mace bata tashi ba.

 

Ya watsa rundunar

Sauro a yau bamu ji shi ba.

 

Bana nufin guda da dai

Ban daura niyyar yinta ba.

 

Amma dalili ya saka, ni

Na yi ta ban shiryeta ba.

 

Domin saboda farin ciki

Dadin zamanmu da kai Uba.

 

Zai sa ni Kwalla yar kadan

Watakil bakwa zarge niba.

 

Sirri na kokon zuciya

Fuska bata rasa jin sa ba.

 

Yururui! A yau na randama

Kodai da ban sabeta.

 

Amma akwai Magana daban

Da ba zan iya ban yi taba.

 

Domin ta nai mini kaikayi

Na zo ka sosa wajen Uba.

 

Najasa da ke yi barkatai

Haka nan butsa! An zuzzuba.

 

Ba kariya ko yar kadan

Daga baya har ya zuwa gaba.

 

Ka ga sangamemen saurayi

Bama su yara kanana ba.

 

Ya yaye al’aura a fi

Li bada jin kunyarsa ba.

 

Wannan abin bisa gaskiya

Ban samu jin dadinsa ba.

 

Domin akwai ill agama

Baki ba za su yabe mu ba

 

Harma sukan zarge mu ne

Ba wai bane, ba inke ba.

 

Ni naji sanda suke fade

Kuma na gwada na jarraba.

 

Kasan ni kan fita ne waje

Zancenga ban kage shi ba.

 

Wannan ta ja mini damuwa

Na tafo ka maganta Uba.

 

Ai ya kamata ka tsawata

Kuma kar a kara nan gaba.

 

Nasan ka baka rurumi

Kuma baka lalaci Uba.

 

Me maida kai kake mai kula

Ga abinda duk ka saka gaba.

 

Tsuguna da tashi ba’a yin ta

A ofishin malam Uba.

 

Baka shiri da munafuki

Cece-kuce baka ji shi ba.

 

Kowa shigo da maganganu

Mara sa shiri a gaban Uba.

 

Kudarsa zai kuwa dandana

Dadin karon bai ji shi ba.

 

Su kwaramniya da rigingimu

Da hayaniya an zuzzuba.

 

Duk dai a karata dole ne

Ayi gaskiya a gaban Uba.

 

Domin kurum shi kayi shi ji

Kowa abinda ya rattaba.

 

Suna daban yau zan fada

A gareka yau malam Uba.

 

Kere kana fasa kan maki

Bin gaskiya baka san shi ba.

 

In kun tuna nace da ku

Guda bana rika yin ta ba.

 

Amma fa har haka dan ku ji

Dadi bazai inganta ba.

 

In banda an ware shi an

Yafa shi an more shi ba.

 

Kash! Nan wajen zan dakata

In sa alama sai gaba.

 

Ni ne Akilu Aliyu na

Gaisheka mai daraja Uba.

 

Kantoma huta lafiya

Sai lokaci wani nan gaba.

 

In Rabbana ya kaddara

Mana saduwa ban mata ba.

 

Bana yawaita maganganu

Sai addu’a zan kattaba.

 

Ya Rabbi ya Sarki Gwani

Allah ka ja zamanin Uba.

 

Amin saboda abin biya

Da yabo Muhammadu Mujtaba.

 

Tamat bi AunilLahi mun

Bidi taimako nasa tun gaba.

 

An dauko daga zauren www.shairai.blogspot.com. Marigayin ya rubuta wakar da rubutun ajami ne, inda daga bisani Malam Fatuhu Mustapha ya maida ta da rubutun boko.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: