DSS Sojoji Da Sun Damke Mai Hada Bama-bamai A Gombe

Gamayyar Jami’an tsaro na Sojojin, ‘Operation Lafiya Dole,’ da kuma Jami’an tsaron farin kaya na DSS, da suke yaki da ta’addanci a shiyyar Arewa maso Gabas, sun kama wani dan ta’addan Boko Haram, wanda ya kware wajen iya hada Bamabamai ga ‘yan ta’addan.

A cewar Kakakin rundunar ta, ‘Operation Lafiya Dole,’ Kanar Onyema Nwachukwu, cikin wani bayani da ya saka ranar Talata a Maiduguri, dan ta’addan, Adamu Hassan, da ake wa lakabi da, Baale, ya shiga hannun jami’an tsaron ne a Kaltungo, ta Jihar Gombe, a daidai wajen binciken da rundunar ta kafa kan hanyar Bauci zuwa Gombe.

“A daya bangaren kuma, Jami’an tsaron na, ‘Operation Lafiya Dole,’ tare da hadin gwiwar ‘yan banga, sun farmaki wasu gungun ‘yan ta’addan na Boko Haram, da suka fantsama domin neman abinci da kayan aiki a garin Kudiye, da ke kan hanyar Dikwa zuwa Gulumbagana, ranar Litinin da yamma.

“Duk tawagogin ‘yan ta’addan hudu, Jami’an tsaro sun kama su sakamakon wani bayanin sirri da muka samu, wanda ya tabbatar mana da cewar, ‘yan ta’addan suna kan hanyan zuwa su wawashe garin.

“’Yan ta’addan sun tabbatar da cewa, su ‘yan bangaren Boko Haram ta Abubakar Shekau ne, tuni Jami’an tsaron suka yi awon gaba da su zuwa ma’ajiyar su, inda suke ci gaba da samun wasu sabbin bayanan daga gare su. Hakanan, Sojojin sun kama wasu Babura biyu, da buhunan abinci da Tamarin daga ‘yan ta’addan.

“Hakanan, Sojojin da ke aikin raba yankin da ayyukan ‘yan ta’addan, a jiya sun kashe wasu ‘yan ta’addan na Boko Haram uku, da suka gudo daga farmakin da Sojoji ke kai ma su a dajin Sambisa, a wasu arangama guda biyu da suka yi da su, a tsaunukan yankin Bokko Hilde, da ke kan hanyar Ngoshe zuwa Pulka da kuma Mujigine, Sojojin sun kwato bindigar AK 47 Guda biyu da kuma babur guda daga ‘yan ta’addan.

Exit mobile version