Daga Khalid Idris Doya,
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya wato DSS, ta bayyana cewar ta bankado wani shirin haifar da rikicin addini a sassan Nijeriya wanda wasu marasa hankali ke yunkurin haifarwa.
A sanarwar manema labarai da Kakakin DSS, Dakta Peter Afunnaya ya fitar a jiya Litinin, ya saida cewar jihohin da masu wannan nufin suke hara sun hada da jihar Sokoto, Kano, Kaduna, Filato, Ribas, Oyo, Legas da wasu jihohin kudu maso gabas don haka ne suka nemi jama’a da su kasance a ankare.
Ya ce; “DSS ta na mai ankarar da jama’a yunkurin wasu marasa kan gado na kokarin haifar da rigicin cikin gida na addini a sassan kasar nan. Jihohin da lamarin ya kunsa sun hada da Sokoto, Kano, Kaduna, Filato, Ribas, Oyo, Legas.
“Kan hakan, mu na jawo hankalin ‘yan Nijeriya da su kaurace wa tsauraran akidun da ka iya tunzura su farmakar wasu.
“A bisa hadin kai hukumarmu da sauran bangarorin tsaro, mu baiwa jama’a tabbacin za mu yi kokarin tabbatar da tsaro da wanzar da komai bisa kan oda, sannan, masu wannan shirin muna gargadinsu da su sauya domin wanzuwar zaman lafiya, tsaro da cigaban kasa,”
“Muna kuma kiran jama’a da su kai rahoton duk wani da suke zargi da kokarin jawo wa zaman lafiya nakasu domin daukan matakan gaggawa,” inji DSS.