Connect with us

RAHOTANNI

Dubbai Sun Halarci Jana’izar Laftanar Habibu Abubakar Usman

Published

on

A ranar Talata ne aka gudanar da sallar jana’izar Laftana Habibu Abubakar Usman, wanda ‘yan bindiga su ka kashe a wani kwanton bauna da su ka yi wa sojojin Nijeriya a wani daji da ke karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina a lokacin da sojojin su ke kan hanyarsu ta komo wa gida bayan sun sami nasarar fatattakar ’yan ta’addan daga wasu maboyansu da ke yankin.

Jana’izar wacce aka gabatar da ita a kofar gidan mahaifin Marigayi Laftana Habibu, da ke Unguwar Sanusi Kaduna, da misalin karfe 10:00 daidai na ranar ta Talata, ta ja hankalin al’umma masu dimbin yawa wadanda su ka halarci jana’izar daga garin Kaduna da kuma wasu garuruwan masu yawa musamman a nan Arewacin kasar nan.

Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu da kuma nu na jimaminsu a kan rasuwar ta Laftana Habibu, in da kowa ya ke fadin halayen kirkin da ya sani dangane da marigayin da kuma irin kwazo da dagewarsa wajen ganin an raba kasar nan da matsalolin tsaro daban-daban da su ke addabar al’umma a halin yanzu.

Da ya ke magana jim kadan daga dawowa makabarta wajen suturta marigayin, Malam Abubakar Usman Sharif Usmaniyya, a kan rasuwar dan na shi ya fara ne da cewa, “Alhamdu lillahi,  Inna lillahi, wa inna ilaihi Raji’un, duk yanda Allah Ya so haka ya ke yi, mutuwa daya ce, sai dai sanadinta suna da yawa. Baccin cewa lokacinsa ne ya yi ba, amma idan da wasu marasa imani ne da Allah sai su ce abin da ya faru din wani shiri ne aka yi domin a halakar da shi. Domin yana Enugu ne sai aka yi masa canjin wajen aiki zuwa Katsina, daga can Katsina din ne kuma aka yi masa canji zuwa Faskari, a bayan da Faskarin ne ta yi kyau kuma aka sake yi masa canji zuwa can Batsari din.

A Batsari din ma aka ce an yi masa canji ya tafi Kwas a Ilori, amma sai ya kasance daga Enugu din ba su aiko da takardar cewa ya tafi Ilori din ba, alhalin duk abokanan Kwas din na shi har sun isa can Ilori din. A kan hakan ne aka yi ta kai komo a kan tafiyar na shi Enugu su ce wannan Abuja kuma su ce wancan, har ta kai shi Kwamandan na shi ya ce za a canza, a karshe dai har su ka aiko da wanda zai canje shi a nan Batsarin, sai dai kuma ba su aiko da takardar tafiyarsa Ilori din ba.

Sannan abin mamaki ma shi ne yanda aka yi ta samun canjin ranar da aka ajiye cewa za su kai farmaki a kan su ‘yan bindigar, in da aka yi ta sanya rana har sau uku ana canzawa. Har sai da ma shi kansa zuciyarsa ta nu na masa rashin jin dadinsa a kan hakan, wanda hakan ne ya sanya ya kiramu yana cewa yana son mu gafarta masa domin shi hankalinsa ba a kwance ya ke ba. a karshe dai shi ne a ranar Asabar aka shaida mana cewa Allah Ya yi masa rasuwa.

A karshe, Usmaniyya ya yi addu’ar Allah Ya karbi shahadar dan na shi, domin kamar yanda ya ce, Malamai sun ce duk wanda ya mutu a kokarin kare kasarsa da jama’arsa shahada ne ya yi.
Advertisement

labarai