Dubban mutane sun yi zanga zanga a duk fadin kasar Togo a ranar Larabar makon da ya gabata, suna bukatar kawo karshen mulkin shekara da shekaru da shugaban kasar Faure Gnassingbe da iyalinsa suke yiwa kasar.
Shugabanin jam’iyyun masu hamayya na kasar ne suka bukaci dubban mutane da su fatsama titunan Lome babban birnin kasar da wasu biranen kasar, su bukaci shugaba Gnassinge ya sauka daga kan ragamar mulki, bayan wa’adinsa ya kare a shekara ta 2020, idan Allah ya kaimu. Haka kuma sun bukaci a yiwa tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin kayyade wa’adin mulkin shugaba.
A shekarar 1992 aka zartar da wata doka da ta yi tanadin wa’adi biyu wa shugaban kasa, to amma mahaifin shugaba Gnassingbe, marigayi Gnassingbe Eyadema ya soke wannan doka bayan shekaru goma.
Zanga zanga makamancin wannan da aka yi a watan Augusta ta buge da zama tarzoma har ma jami’an tsaro suka kashe mutane biyu
A shekara ta 2005 shugaba Faure Gnassingbe ya dare kan ragamar mulki bayan rasuwar mahaifinsa wanda ya share shekaru talatin da takwas yana jan ragamar mulkin basar Togo. A ranar Talatar makon da ya gabata ne dai Majalisar Ministocin kasar tayi na’am da wata shawarar da aka gabatar na mayar da kayyade wa’adin mulkin shugaban kasa.