Connect with us

LABARAI

Dubun Mai Yi Wa Jarirai Fyade Ta Cika A Jihar Nasarawa

Published

on

Hukumar fari kaya NSCDC ta kasa reshin jihar Nasarawa ta gabatar da Ahmadu Yaro mai sana’ar Fyede ga jarirai da kananan yara a jihar Nasarawa.

Da yake jawabi ga manema labarai mataimakin Kwamandar NSCDC Mista Obeh Oka ya shedawa manema labarai cewa shi Ahmadu Yaro dubusa ta cikane a lokacin da yayiwa wata jaririya yar wata 4 da haihuwa fyede.

Ya kara da cewa Ahmadu Yaro yayiwa  Jaririya mai suna Rukayya Aliyu Fyede a ranar 27-5-2020 a garin Adogi dake karamar hukumar Lafia cikin jihar Nasarawa.

Sannan Runfunar farin kayar ta cafke Ahmadu Yaro ne a ranar 22-6-2020 da misalin karfe 2:30am a garin Adogi.

Ya ce a binciken da mukayi masa ya tabbatar da cewa ba akan wannan yarinyar ya fara wannan mummunar aiki ba. Ya taba aikata irin wannan aiki ga yara kanana da yawansu ya kai hudu.

Ya ce, Ahmadu Yaro yana daukar kananan yaran ne cikin dare ya kaisu Makarantar Sakondire yayi lalata dasu ya tafi ya barsu cikin jini.

Yarin yar da Ahmadu Yaro yayiwa Fyede a baya bayan nan yar wata hudu sai da aka kaita Babban Asibitin koyarwa ta Jam’ar jihar Pilato dake garin Jos. Kuma anyi mata aiki a hanjin ta.

Da yake amsa tambayar manema labarai wanda ake zargin Ahmadu Yaro ya amsa cewa yayiwa yarin yar Fyede kuma yana tabbatar da cewa wannan shine na karshe ba zai sake ba.

Iyayen yaran da Ahmadu Yaro yayiwa Fyede sun shedama Wakilinmu yadda lamarin ya faru.

Mahaifiyar Rukayya Aliyu mai suna Maimuna ta sheda cewa tana kwance tare da Jaririyar suna barci tsakiyar dare misalin karfe uku ta farka sai bataga Jaririyar ba. Ta duba ko ina bata ganta ba.

An bincika ko ina cikin gidan su amma ba a ganta ba. Sai aka bazama yawon nimanta aka ganta tana kuka kwance cikin jini a Makarantar Sakondire.

Bayan munzo da ita Asibiti akace sai dai muwuce zuwa Jos a nane akayi mata tiyata. Sai da aka bude cikin ta akayi tiyata hanjinta sun fita.

Mun samu taimako daga kungiyoyi dama Gwamnatin jihar Nasarawa ta gurin uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat Abdullah Sule.

Itama malama Zainab tana daya daga cikin iyayen yaran da akayiwa fyeden tace ga yarta nan yar shekara daya da wata biyar. Tace “muna kwance a daki muna barci da na farka cikin dare sai banga yarinya ba na duba dakunan matan gidan bamu ganta ba. Nayi kururuwa jama’a sun taru munyi ta dubawa bamu ganta ba. Yan Bangan unguwa sun zo suna dubawa sai sukaji ihu da sukaje ta wurin da ake kuka sai ya jisu ya gudu sun bishi amma basu kamashi ba, an dauko yarinya ya daure mata baki da gyale jikinta da kayanta sun baci da jini”. Inji Zainab.

Itama Malama Aishatu Haruna ta shedama wakilinmu cewa yarin yar ta mai suna Amina Haruna ta fada tarkon Ahmadu Yaro lokacin tana Jaririyar yar wata tara muna kwance a gado da Daddare. Na farka amma banga yarinya ba. Ayi ihu jama’a sun taru anyi ta dubawa har gari ya waye amma ba a ga yarinya ba. Sai daga baya aka tsinceta a makaranta kwance cikin jini anyi mata Fyede.

Itama Shamsiya Abdullah  mahaofiyar Aisha Abdullah Wanda ake zargin Ahmadu Yaro yayiwa Fyede tace, mahaifin yarinyar ya rasu tun tana da wata biyu a ciki ba a haifeta ba . bayan na haifeta tana da wata biyar a Duniya cikin dare misalin karfe uku nayi ihu jama’an gida suka fito NA sheda masu an sace jaririya  munyi ta nimanta  maza suna ta yawo suna nimanta da akaje hanyar unguwar Ayaba a nan aka ganta an lulubeta da ganye, jinkinta duk jini.

Munyi jinya a Asibitin Dalhatu Arfa dake Lafia. Bayan munyi jinya da ta warke ranar da muka koma gida washe gari ya sake kawo farmaki nayi masa ihu ya gudu yabar takalminsa da wayan hannu.

Nace nayi kararsa aka ce muyi shuru tunda ba a kamashi a hannu ba . kuma da wannan Azumin ya sake zuwa gidanmu da daddaren.

Ma’aikatan jin dadin mata da walwala ta jihar Nasarawa ta nuna damuwa kan lamarin da ya faru da wannan karamar yarinya.

Kwamishiniyar harkokin mata Hajiya Halima Ahmad Jabiru tace, Gwamnatin jihar tayi tsaye kan lamarin sai anyima wanda aka samu da hannu ciki mummunar hukunci wanda zai zama darasi ga na baya.

Tace , kuma ba za su bari shari’ar ta sha ruwa ba . saboda tun lokacin da Gwamnati ta samu labarin wannan mummunar aiki ta sanya duk yadda za a yi a duba ayi bincike a zakulo wadanda ke aikata wannan aiki. Cikin ikon Allah an kamashi to zamubi shari’an mu tabbatar anyi hukunci mai tsanani.

Dama aikin ma’aikatanmu ce kuma ba zamu bari ba

Kwamishiniyar ta zargi iyayen yaran da tsuke baki da sukeyi shine ya ke kawo yawaitar Fyede a yan kunan. Tace “suna yin suru suki fada wai saboda kunya amma yanzu muna kara wayar masu da kai da zarar anci zarafinsu ko yaransu su fito su fada za’adauki mataki na gaggawa”.

Ta kara da cewa yanzu Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki nauyin jinyan yarin yar , dama nauyin iyayen. Duk da cewa Gwamnati bata samu labarin abin da wuri ba sai da iyayen sukaje Asibiti a Jos amma yanzu duk wani takardan Asibiti Gwamnati ta dau nauyi.

Advertisement

labarai