Dubun Masu Safarar Makamai Ta Cika A Zamfara

Daga Hussaini Yero,

A kokarin da Runundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara keyi hadin gyuwa da Rundunar, Dakarun FIB da STS da Sufeto janar Alkali ya turo Karkashin jagorancin DSP , Hussaini Gimba,mun samu nasarar kama Fatima Lawai da ke safarar alburusai daga Gada Jihar Sokoto zuwa Dan Jinga cikin Karamar Hukumar Tsafe a Zamfara.

Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Zamfara, CP Ayyuba Elkana ya bayyana haka ne aloakcin da yake gabatar da wadanda aka kama agaban “Yan jaridu a Hedikwatar su da ke Gusau.

CP Ayyuba Elkana ya bayyana cewa, Rundunar sa Karkashin jagorancin Hussaini Gimba,ta samu nasara kama Fatima Lawal da take safarar Makamai da harrasai ga Kwamadan ‘Yan Bindiga na Jihar Zamfara da Katsina Aleru .Kuma mun kamata da harsasai masu rai 993,zata kai ma Shugaban ‘Yan Bindiga Aleru da yake a yankin Dan Jibga.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa,Buba Abubakar Shima mun kamashi ya na yima masu Satar Shanu da masu garkuwa da mutane rahotan Siri a yankin magani cikin Karamar Hukumar Gusau.

Kuma da zarrar mun kammala binciken mu zamu turasu gaban Kotu dan yanke masu hukunci.inji Kwamishina Ayyuba Elkana.

Fatima Lwali ta bayyana ma.”Yan jaridu cewa,lallai an kamata da harsasai 993, kuma Samaila mijin kanwarta ne ya sanya cikin harkar, Kuma ya bani dubu hamsin ta farko kuma bayan takai masu makaman sun karanata dubu talatin.kuma kaddace ta sanya wannan aikin.ijita.

Shima Buba Mai bada rahotan Siri ya sheda ma “Yan jaridu cewa, Kaddarace ta sanya na kira masu satar shanu zuwa magami da wasu garuruwan Dan syi sata kuma sunyi Babu abinda suka bani.dan haka nake rokon hukuma da ta taimaka tayi mani afuwan.

Exit mobile version