Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A cikin satin nan ne ‘yan kato da gora a jihar Bauchi suka yi nasarar cafke wasu barayi mutum shida da suke shiga gida-gida suna kwace da satan kaya da dukan jama’an da suka tarar a duk gidan da suka shiga suka rasa abin da suka je nema wato kudi ko makamancinsa, a wani lokacin ma har saran mutum suke yi da adda ko da wuka.
Isa Jibrin Makama shugaban ‘yan kwato da goro (‘yan kwamiti) ya bayyana wa manema labaru cewar sun yi nasarar cafko miyukun ne a wani sabon unguwa da ke bayan filin jirgin sama, inda ya ce kai tsaye suna garzin wadanda suka kama ne da fashi da makami “da bakinsu sun shaida mana cewar sun shiga gidaje sama da hudu sun kuma Sassari wasu mutane ga wasu daga cikin wadanda aka sara zaku iya ganinsa wani sun saresa a kai wani hanu da dai sauran wuraren da suka illata mutane. Mun kuma kamo su ne a bayan gari da ke Bauchi”. In ji sa
Daga bisani ya bayyana cewar suna kan bincikesu da darar suka kammala za su hannantasu ‘yan fashin ga hukuma, da yake bayyana abubuwan da suka iya kamowa a hanun miyagun ya ce sun samesu da wuka da kuma addina.
Abdulmakin daga unguwar Inkil yana daga cikin wadanda suka shiga hanun ya amince da laifinsu sai ya bayyana cewar sun saci wayoyi a gidajen jama’an unguwar da kuma saran wasu ya tabbatar wa manema labaru wannan “Idan ka ga mun daki mutum har mun ji masa ciwo to idan muka shiga gidanka muka yi sata kai kuma ka yi kokarn biyu mu, to mukan doki mutum har mu ji masa ciwo”. In ji Barawon
Iliyasu daga unguwar Kurmi a Darazo ya bayyana cewar dubunsa ta cika ne bayan da ya zo wajen abokinsa hutun sallah, ya amsa dukkanin laifin da ake zarginsa da aikata wa na sata a gidanjen mutanen Bauchi. Ya roki da a sausauta musu wajen hukunci ganin cewar bai taba aikata laifin ba.
Shi ma Ahmad daga unguwar Yakubu Wanka ya ce sun je unguwar ne domin yin satar waya da dan abubuwan da suka gani.
Baba Alhaji wanda ya fito daga jihar Gombe ya ce sun je bayan Airport din ne domin yin kwacen wayoyi da kuma dukan wanda ya kawo musu tangarda.
Wakilinmu ya labarta mana cewar wani abin takaici daga cikin wadanda aka kama hard a wata budurwa mai suna Aisha wacce ta zo daga jihar Gombe inda ta shaida mana cewar ta biyo saurayinta ne Bauchi daga bisa aka kamasu a unguwar Bayan gari (inda karawai ke sheke ayarsu) da muka tambayeta alakarsu ta bayyana cewar soyayya ne a tsakaninsu, amma ba aurensa zata yi ba domin yanzu haka ma akwai wani wanda ya kawo sadakinta da kuma kayan aurenta, ta bayyana cewar shi dai wannan din tana sonsa ne kawai. Ta bayyana cewar ita bata daga cikin barayin kuma bata san komai kan yanda suke kitsa yin satarsu ba, amma ta amince kan cewar iyayenta basu san ta zo wajen wannan saurayin dga Gombe ba. ita dai Aisha wacce yanzu haka ta shiga dumuwa ta bukaci da ‘yan kwamitin su suketa a cewarta ita ba barauniya ba “iyayena ba zasu aura min shi ne bane domin baida sana’a ni kuma ina sonsa, shi ya san a biyu sa nan garin, amma akwai wanda shi ne zai aureni”. In ji ta
Wasu mutanen unguwar da muka zanta da su, sun bayyana damuwarsu kan yanda barayi suka maida unguwarsu na bayan Air Port wajen cin kasuwarsu a cewarsu hakan ya faru ne sakamakon unguwar tasu sabuwace.
Abubakar G. Sambo da Isma’il Usman su ne wadanda barayin suka lakkada wa duka, suka kuma jikkata sun bayyana cewar har cikin gida barayin suka biyu su suka yi musu wannan mummunar ta’adin.