Dubun Wasu Barayin Motoci Ta Cika A

Jihar Nasarawa

Daga Abubakar Abdullahi, Lafia

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wani gungun barayin motoci tare da kama wata karamar mota kirar ‘Camry’ a hannunsu. Mai magana da yawun rundunar Idreesu Kennedy, ya tabbattar da haka a lokacin da ya ke zantawa da ‘ manena labarai a birnin Lafia. Kennedy ya kara da cewar, “Rundunar ta samu bayanai da dama cewa wasu barayi su uku dauke da bindigogi suna tare mutane a hanya suna karbe masu motoci a jihar,  shi ya jami’an rundunar suka shiga bincike inda aka yi nasarar cafke miyagun a ranar Asabar da ta  wuce”.

a ce, an kama biyu daga cikin barayin ne a yankin Masaka ta Karama Hukumar Karu sai dai daya daga cikinsu ya tsere, amma  y ace, za su bi sawunsa har sai sun zakulo shi duk inda ya shiga. Ya kara da cewa, “Mota kirar ‘Camry Bulldog’ da muka kama a hannun barayin, mallakar wani mai suna Yusuf Manga ce wadda aka sace ta a ranar 21 ga watan Satumban 2017”.  Jami’in  ya bayyana cewa za a mika barayin ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike, tare da bayyana sunayen barayin kamar haka; Nasiru Danjuma da Collins Osagye na Unguwar Zakara a yankin Uke na Karama Hukumar Karu. A karshe, ya ce da zarar rundunar ta kammala bincikenta za ta gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo.

Exit mobile version