Connect with us

LABARAI

Dubun ‘Yan Kungiyar Asiri 51 Ta Cika A Anambara

Published

on

Dubun wasu ‘ya’yan kungiyoyin asiri biyu da ba su ga-maciji-da-juna ta cika yayin da rigima ta barke a tsakaninsu a Aukwa, babban birnin Jihar Anambara.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar  Anambra Garba Umar, ya sanar da cewar, sakamakon musayar wutar da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar asirin biyu, ‘yan asirin su goma sha shida sun bakunci lahira, kana daga bisani jami’an tsaro suka cafke wasu 35.

Umar wanda ya sanar da hakan a ranar talatar da ta gabata lokacin da yake baje kolin ‘yan kungiyar asiri biyu da suka yi kaurin suna a yankin, da ake kira Black Ade da Bikings Fraternity.

Kwamishin ya baje kolin wadanda ake zargin su talatin da biyar ne, a harabar rundunar, inda ya yi nuni da cewar ayyukan ‘yan kungiyar yana kara kazanta a yanikin na Akwa, inda hakan yake kara jefa tsoro a zukatan al’ummar yankin, musamman ganin cewar, kashi casi’in na matasan  Awka, har da dalibai da sauran su ana zargin sun shiga kungiyar asirin.

Kwamishinan ya yi kira ga iyaye dasu rika sa ido akan ‘yayan su da wadanda suke riko, ganin cewar rundunar zata fara tura yaran Kotu don yanke masu hukunci.

Umar ya jaddada cewar, rundunar ba zata rungume hannu ta, ta bari  ana aikata ayyukan asiri  a yankin ba.

Wasu daga cikin ‘yan kungiyar da aka baje kolin su, sun hada da,Chukwudi Machie  shekara 34 da Chukwudi Igwebueze mai shekaru 32, da Onyeka Igbanugo  shekara 28 sai  Ifeanyi Anazoba shekara 32, da kiuma  Chukwuemeka Nwokoye  shekara 32 .

Daya daga cikin wadanda ake zargin  Chukwudi Machie a hirar sa da manema labarai ya amsa laifin sa, inda yace, mafi yawancin ‘yan achaba da masu tuka keke Napep a garin kashi casa’in ‘yan kungiyar asiri ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: