Duk Abin Da Za A Kera A Chana, Za Mu Iya Yinsa A Kano —Alhaji Rafani

Kasuwar kera tukwane ta Bachirawa da ke Kwanar Ungogo a jihar Kano, ita ce kasuwa ta farko a Arewa da ake zuwa daga sassa da dama na ciki da wajen kasar nan domin harkar tukwane. Kasuwar wata makera ce kuma masaya da ke tallafa wa ci gaban jihar Kano. Jaridar LEADERSHIP A YAU ASABAR ta sami tattaunawa da Shugaban kungiyar masu kera tukwane na jihar Kano, ALHAJI RAFANI SULAIMAN ABDULLAHI, wanda ya shaida mana tarihin kafuwar kasuwar kasuwar da gudummawar da take bayarwa ga al’umma. Ga yadda hirar ta kasance.

Muna so ka gabatar da suna da matsayinka a wannan kasuwa?

Salamu Alaikum. Sunana Rafani Sulaiman Abdullahi, shugaban kungiyar masu kera tukunya ta jihar Kano da ke Bachirawa Kwanar Ungogo. Yaya aka soma tukunya a wannan kasuwar?

Tarihinta yana da yawa, domin tun daga Kasuwar Sabongari da iyaye da kakanninmu, kusan gadarta muka yi sana’ar. Kuma duk abin da sana’a ke yi wa dan’adam, wannan sana’a ta yi mana shi, ta yi mana riga da wando, duk abin da Allah yakewa dam’adam a sana’a dai ta yi mana a wannan. Ka ga akalla ni dai na kai kusan shekara 30. Ina wannan sana’a na yi aure na yi iyali, da ita na yi gida, haka ma Sakatarena wanda a yanzu ma hedimasta ne na makaranta, kuma yana wannan sana’ar bai yarda  ita ba, yana da kanne wajen 15 ya kawo su, shi yake kula da su da wannan sana’a. ka ga kuwa abin da ya yi maka wannan ba abin da ya fi shi a sana’a ta hannu.

 

Ka ce ta somo ne daga Kasuwar Sabongari. To kai a nan ka soma sana’ar ko daga can ka soma?

Ai, tun ban fi shekara 15 ba na soma wannan sana’ar, in je makaranta in dawo, ka ga kuwa gadarta muka yi ke nan.

 

Wato ke nan kai ma kana kera wannan tukunya?

Ni dila ne kuma mai kerata, ina bada kudi a tafi sassan kasar nan daban-daban a saya min alminiyan, ko mu sa yi kayayyaki mu narka mu sami alminiyan. Sannan akwai mutanenmu  na Chana da Indiya suna zuwa muna yi masu Ingot, wato mulmulallen alminiyan, suna fita da shi kasashen Turai. Abin sha’awa duk wani matashi da yara da suke makwabtanmu sun koyi wannan sana’a, kusan babu mai zaman banza a cikinmu domin wannan makwabtan akwai yara sama da 200 a Bachirawa suna wannan sana’ar.

Wani abin alfahari ma a yanzu, saboda yanzu gari ya tarar da kasuwa, akwai irin wani dan hayaki da sauransu, to karamar hukumar Ungogo sakamakon zuwan wannan Kantoma, Alhaji Aminu Kabara, kusan shekara hudu muna Shari’a da makwabta, yanzu ya tabbatar mana da sabon wuri da ya ba mu a karamar hukumar Ungogo.

 

To, ya sunan wajen da kuka ce an bakun?

Sunan wajen da aka ba mun, Bugujum.

 

Wannan ya nuna za ku sake fadada kasuwar ke nan?

A’a, fadadata za mu yi sakamakon gari ya zo wajen ya dan yi mana kadan, sakamakon ganin matsaloli da muke samu, kuma can ma da za mu koma mun sami Dagaci a kan ya kawo yara domin a rika koya musu wannan sana’ar domin in ka ce aikin gwamnati za ka yi. A kasuwar nan akwai mai NCE da Diploma har Digiri, amma wannan sana’a suke yi, to ka ga abin alfahari ne, wajen ya riga ya sami dan matsi za mu kuma koma wancan wurin.

 

A jihar Kano kukan samar da damar sana’a ga matasa kamar guda nawa?

A kalla duk shekara  muna yaye matasa guda 150 ko 80, ya danganta da mutanen da suka kawo ‘ya’yansu ya gama karatu ko yana zaman banza. Kuma abin alfahari ma in ka zo kana shaye-shaye, to in sha Allahu za ka daina, sakamakon samun sana’a,  za a kula da kai, to ka ga abin alfahari ne ga gwamnatin Kano, wannan ci gaba da ake samu.

 

Wadanne irin matsaloli kuke fuskanta a wannan sana’ar?

Matsaloli dai ba a rabuwa da su. Kamar yadda na gaya maka, matsalar mutanen  Unguwa da suka zo suka samemu, shekarar mu 24 a nan kasuwar, lokacin wurin na daji, amma sakamakon zuwan wasu mutane suka ce ana damunsu da hayaki, to mu masu bin doka da oda ne, shi ne muka garzaya kotu, kotu ta zo ta duba har muka kai kusan shekaru shida muna Shari’a. Sakamakon wannan abu, wanda mu nasara muka yi, dama wajen ya matse mana, mutanenmu har sun soma fita wasu wurare suna samun kwangaye. Akwai kasashen Afirka kamar Nijar, Ghana, Kamaru  da sauran kasashe suna zuwa suna sayen wadannan tukwane ana lodawa a mota hudu kusan duk wata ma dora tirela daya, abin alfahari ne a ce sana’ar hannu da ake zuwa daga kasashen Duniya ake saye.

Saboda haka ita gwamnati sai ta duba, ba saya muka yi ba, ta ba mu wannan wuri don ci gaban Kano da al’ummarta. Ina kira dai ga gwamnati, mai sana’ar hannu yana da muhimmanci, dogaro da aikin gwamnati shi yake kawo zaman banza, amma idan tana tallafa wa masu sana’ar hannu irimmu, to duk matsaloli za su ragu.

 

Da yake na fahimci aikinku na yau da kullum ne, a kullum kukan fitar da tukwane nawa?

Akalla mukan fitar da tukwane sama da 3,000, tunda kasuwa ta Allah ce, wata rana ma a kan saida sama da 5,000 ma.

 

To bayan tukwane akwai wasu kere-kere da kuke ne?

Sosai ma kuwa, akwai ruma-rumai na mota, da safaya fat, ga shi nan duk abin da ka kawo za a yi maka shi, kuma ya fi na Chana inganci. Akwai Inyamurai da a nan suka koyi fasahar nan har ta kai sun je jihohinsu suna cin gajiyarta.

 

Wannan yana nufin ke nan da Gwamnati za ta ba ku tallafi, za ku iya samar da kayayyakin da ake shigowa da irinsu?

To kullum abin da Gwamnati ita ya kamata ka tallafawa, saboda Allah ya ba mu karfin jari a kawo mana kayan aiki ingantattu, to wallahi duk abin da za a yi shi a Aba ko Chana, to za mu yi shi a Kano. Ka ga muna yin kan fanfo, da ruma-rumai na mota, hauzin da banten filet na mota, amma mun dauka mun kai wa Inyamuri ya goge mana, to ka ga matsala ce wannan.

Amma da a ce Gwamnati za ta tallafa mana da kayan aiki, muna da matasa ’yan boko wadanda za su iya sarrafa injunan. Muna kira ga Gwamnati ta tallafa mana da kayan aiki, ba kudi ba, mu za mu tallafa mata ta biyan haraji. Alhamdu lillahi a kasuwa muna tallafa wa Gwamnati da biyan haraji da rage masu zaman kawai.

Duk wata kungiya da za ta taimakawa da wannan Gwamnati da wannan, ya kamata Gwamnati ta kalleta, amma da cokali ba ta gaza tallafa mana ba, amma muna bin ka’ida ta Gwamnati, in banda zuwan  wannan Kantoma na Ungogo, Alhaji Aminu Kabara, wanda muke fata Allah ya saka masa da alkhairi, domin ya kalli domin ya kalli kukanmu ya tallafa mana, Allah ya kara masa daukaka, domin za a samu ci gaba.

 

 

Exit mobile version