Duk Da Bashin Naira Biliyan 120 Da Muka Gada Mun Samu Nasar Bunkasa Gombe – Gwamna Inuwa

Bunkasa Gombe

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa duk da dimbin kalubale da gwamnatinsa ta ci karo da su daga hawan ta kan karaga shekaru biyu da suka gabata ciki kuwa har da samun bashin sama da naira biliyan 120 da gwamnatocin baya suka bar masa, gwamnatinsa ta samu nasarar samarwa jihar ci gaba ta hanyar damawa da kowa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabin ga dandazon jama’a a cikin wasa na Pantami yayin bikin cikarsa shekaru biyu da hawa kan karagar mulkin Jihar Gombe.

Ya ce cin wannan rabin wa’adi wani muhimmin lokacin ne na tuna yadda aka faro tafiyar raya jihar ta Gombe, “Idan za ku iya tunawa lokacin da muka karbi gwamnati a rana mai kamar ta yau a 2019, mun gaji dimbin matsaloli da suka hada da bashin da ya haura Naira biliyan 120, da lalatattun harkokin ilimi da lafiya, da gurbataccen yanayin aikin gwamnati da kuma watsi da aka yi da yankunan mu na karkara. Yayin da muka kimtsa tinkarar wadannan matsalolin sai kuma aka samu barkewar annobar Korona, da kuma dokar kullen da ta biyo baya, lamarin da ya jefa harkoin lafiya dana tattalin arziki da zamantakewa cikin wani mawuyacin hali a duniya baki daya.

“Hakan kuma ya jefa kasar nan cikin kakanikayin tattalin arzikin da ya shafi jama’a da sana’o’i da ayyukan su. To sai dai bisa addu’o’i, hadin kai da goyon bayan ku, wadannan kalubale basu kawar damu daga kan muradun mu na cika alkawuran da muka dauka ba.”

Gwamnan ya ce a shekaru biyun da suka gabata, gwamnatin sa ta dauki kwararan matakai na magance manyan matsalolin ci gaba dake fuskantar jihar, yana mai tunatar da al’umma kan irin alkawiran da ya dauka a manufofin da tsare-tsaren sa.

“Mun dauki tsarin tafiya da kowa, wadda ya bamu damar cimma gagarumar nasara a kokarin mu na bunkasa tsarin kiwon lafiya, da ilimi daga tushe, da inganta muhalli, da raya karkara, da inganta birane da samar da sauye-sauye a hukumomi dama tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.”

Ya ce Gwamnati mu ta nuna cewa namu ba irin nasu bane, ta hanyar magance almubazzanci da kama karya da kuma gaba irin ta siyasa ya zuwa adalci da sanin ya kamata

“Don cika alkawuran mu na tabbatar da adalci, mun karfafa hukumar kula da kudade da tabbatar da adalci don ta gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata, mun kirkiro dokar kula da kwangiloli, da kirkiro da asusun bai daya da kuma samar da hukumar farfado da aikin gwamnati, wacce ta kirkiro da tsarin tantance ma’aikata a zamanance ta hanyar na’urori masu kwakwalwa, wadda ya taimaka wajen magance matsalolin ma’aikatan bogi da illolin da suke haifarwa.”

“Mun kuma bunkasa yanayin kudaden shigan mu da kimanin kaso 25 bisa dari a bara, da kuma kaso 62 bisa dari a rubu’in farko na wannar shekaru idan aka kwatanta da na bara, mun kuma biya bashin fansho da giratutin da ya kai na Naira biliyan 2 da miliyan 400, wanda hakan ke nuna da cewa akalla muna biyan Naira biliyan 100 a duk wata, daga cikin bashin fanshon da muka gada daga tsohuwar gwamnati da ya kai Naira biliyan 14.”

“A yayin yakin neman zabe, mun yi alkawarin farfado da sashin ilimi ta hanyar kara yawan kasafin kundin sashin da samar da kayayyakin koyo da koyarwa a dukkannin makarantin mu na firamare d sakandare. A zuwan mu ofis, mun ayyana dokar ta baci a sahin, tare da kara yawan kasafin kundin sashin da kimanin kaso 60 cikin dari a 2020 da 2021.”

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, hakan ya haifar da giggina azuzuwan karatu kimanin 584 a makaranti 156, tare da sanya kujeru da kayan aiki a cikin su. Haka nan mun samar da kujerun zama fiye da dubu 30 ga makaranti da cibiyoyin karatu, ga kuma kayan wasanni da na tabbatar da tsabta da kayayyakin aiki a dakunan gwaje-gwaje da sauran kayayyakin aiki da dama.

Ya ce, “Mun kuma kwashe yara fiye da dubu 300 daga kwararo wadanda basa zuwa makaranta, tare da kakkafa cibiyoyi karatun ‘ya’ya mata da almajirai kimanin 676 a karkashin shirin nan na samar da ingantaccen ilimi daga tushe da ake kira BESDA a takaice.”

Ya ce don samar nagartacciya kuma lafiyayyiyar al’umma, “Gwamnatinmu ta dauki matakin bai-daya na farfado da tsarin kiwon lafiya cikin shekaru biyun da suka gabata. A bisa hakan, ta kwaskware akalla cibiyar lafiya a matakin farko guda 1 a kowacce gunduma, cikin gundumomi 114 da ake dasu tare da samar musu kayayyakin aikin da suka wajaba, da hasken lantarki da famfunan burtsatse masu aiki da hasken rana, don hidimawa jama’a ba dare ba rana.”

Gwamnan ya ce a kokarin gwamnatin sa na cika burin ta na samar da muhimman ababen more rayuwa, ta gina fiye da Kilomita 350 na hanyoyin mota a karkashin shirin Network 11-100 wanda yake da nufin gina akalla kilomita 100 na tituna a kowace karamar hukuma guda 11 da suke jihar.

“Hakazalika, an kammala shirye-shirye don samar da dama ga yankunan karkara kan shirin kasuwancin kayan aikin gona (RAAMP) da hadin gwiwar ma’aikatar kudi dana aikin gona ta tarayya don kara bunkasa al’ummomin mu na karkara.”

“Tsarin samar da ruwan sha na yankin Gombe wanda ya samu matsala na tsawon shekaru saboda na rashin kulawa a karkashin tsohuwar gwamnatin da ta shude, an sake dawo da shi wanda yake samar da kusan lita miliyan 50 na ruwa a kullum zuwa babban birni da kewaye. Hakazalika, don inganta samar da ruwa ga al’ummomin dake nesa, Hukumar samar da ruwan sha a karkara da tsabtace shi (RUWASA) ta tona rijiyoyin burtsatse a fadin jihar.

Ya ce noma yana ci gaba da taka muhimmiyar rawa a ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar, kasancewar sa babbar hanyar samun abinci ga yawancin jama’ar jihar. Ya ce Gwamnatinsa ta sami damar bunkasa tallafi ga manoman ta hanyar samar da takin zamani, da iri da sauran kayan aikin gona.

Ya ce jihar Gombe tana da nata matsalar rashin tsaro da ake fuskanta, “Amma dai, an dauki matakai masu ƙkarfi don takaitawa da maido da zaman lafiya da bayar da tallafi ga al’ummomin da abin ya shafa.”

“Za mu rungumi fasahar zamani, mu yi amfani da sabbin tunani tare da kuzarin matasan mu don karfafa wadannan nasarorin. Haka kuma za mu ninka kokarinmu don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, da samar da ayyukan yi da bunkasa kwarewa da damar matasan mu masu tarin yawa. Haka nan, za mu karfafawa matan mu gwiwa da magance matsalolin masu fama da larura a cikin al’ummomin mu.”

Gwamnan ya yaba wa majalisar dokokin Jihar Gombe da bangaren shari’a na Jihar saboda kyakkyawar alakar aiki dake tsakanin su cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata. Yana mai basu tabbacin cewa zumuncin dake tsakanin su zai karfafa.

“Hakazalika, rawar da sarakunan mu suka taka wajen sasanta rikice-rikice da samar da zaman lafiya sun cancanci yabo. Dangane da haka, muna aiki don farfado da cibiyoyin gargajiyar mu domin su taka rawar gani wajen ci gaban Jihar mu. Za mu ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da ayyuka masu mahimanci kamar shirin samar da gidaje masu rahusa guda dubu 2 da 500 da samarwa jihar mu katafariyar sakatariya da zata kunshi ma’aikatu, da hukumomin gwamnati da kuma inganta rukunin majalisar Jihar zuwa matsayi mafi dacewa. Rumbun adana bayanai kan rashin aikin yi da muka samar, zai taimaka mana wajen maye gurbin dukkan guraben da za a kirkira sakamakon ci gaba da ayyukan da ake aiwatarwa a fadin jihar a kokarin mu na samar da damammaki ga matasan mu marasa aikin yi.”

Shi kuma a nasa fannin, tsoron gwamnan Jihar Sanata Muhammadu Danjuma Goje, ya ce a matsayinsa na wadda ya goyi bayan zaben da aka yiwa Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan Jihar Gombe, ya gamsu da irin nasarorin da gwamnan ya cimma kuma ya dora daga inda gwamnatin sa ta ajiye.

Ya ce, “Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bai ba mu kunya ba, ya yi aiki kuma zai ci gaba da aiki don samar da nagaryaccen ci gaba a jihar mu, yana mai kira ga al’ummar jihar su mara masa baya sojin kuwa yana aikin kwarai”.

Ya ce gwamnonin Jam’iyyar APC a shiyyar arewa maso gabas sun yi fice, domin suna maida hankali ne kan abin da ya sa aka zabe su don shi da suka hada da kyautata rayuwar al’umma da samar da ayyukan raya kasa.

Shi ma a nashi jawabin, tsoron gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, ya bayyana Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin kwararren Shugaban dake samar da romon demokiradiyya ga al’umma har gida ba tare da la’akari da banbanci siyasa ba.

Ya ce duk lokacin da ya ziyarci Jihar Gombe sai ya ga sabin nasarorin da ci gaba, yana mamakin irin manufofi da tsare-tsaren da suka kai ga cimma wadannan dimbin nasarori da gwamnan yayi cikin dan kankanin lokaci.

Exit mobile version