Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Duk Da Kalubalen Korona Da Lassa A 2020 Gwamnatinmu Ta Shimfida Ayyukan Raya Kasa, Inji Gwamnan Bauchi

by Khalid Idris Doya
January 3, 2021
in RAHOTANNI
2 min read
Kiran Da Tsohon Gwamna Shema Na A Dawo Tafiyar PDP Ya Makara –inji PDP A Gyara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sanata Bala Muhammad, gwamnan jihar Bauchi, ya lura kan cewa shekarar 2020 ta kasance shekara wacce al’umma ba za su taba mancewa da ita ba bisa kalubalen da ta zo da su na annobar Korona da cutar zazzabin Lassa amma ya ce duk da hakan gwamnatinsa ta yi kokarin shimfida ayyuka raya jihar da daman gaske.

Bala sai ya nuna cewa Gwamnatin za ta sake gami da kara zage damtse a wannan sabuwar shekarar 2021 domin cigaba da gudanar da ayyukan da suka dace wajen ganin rayuwar jama’a ta inganta.

samndaads

A jawabinsa na taya al’umma murnar shiga sabuwar shekarar 2021, Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya yi kira ga al’ummar jihar Bauchi da Nijeriya da su cigaba da zama da junan su lafiya da gudanar da addu’o’in zaman lafiya da tsaro da cigaba me daurewa ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini ko ta kabila ba.

Ya ce bisa kokarin Gwamnatin su duk da kalubalen da shekarar 2020 ta zo da su da suka hada da ibtila’in cutar Korona da zazzabin Lassa, gwamnatinsa ta samu nasarar kammala wasu manyan ayyuka a fannoni daban-daban na inganta rayuwar al’umar jihar.

A cewar sa, zaman kashe wando tsakanin al’umma ya ragu cikin shekarar da ta shude inda ya bada misalai kan tallafin jari da horo kan sana’oin hannu da gwamnatinsa ta samar.

Ya yi bushara wa al’umma musamman mazauna fadar jihar da cewa matsalar karancin ruwan sha na dab da bankwana da zarar aikin fadada samar da raba ruwan ya kammala.

Ya ce ko kusa annobar Korona ba ta sanyaya masa guiwa ba wajen gina sabbin dakunan jinya da kuma sayo manyan na’urorin gwaje-gwaje na zamani don saukaka jinya.

Ya kara da cewa yayin kullen yaki da yaduwar cutar, gwamnatinsa ta kaddamar da ayyukan raya kasa inda ya zuwa yanzu an kammala da dama daga cikin su a birane da yankunan karkara musamman a fannin noma, ilimi, kiwon lafiya da hanyoyi.

A cewar gwamnan, dubban matasa da mata sun samu horo na musamman kan hanyoyin inganta sana’oin hannu na zamani.

Dangane da batun tsaftace da inganta tsarin albashi kuwa, Gwamna Bala ya ce cikin yardar Allah gwamnatinsa na samun yabo kan yunkurin ta na tsamo bata-garin dage zagon kasa ga dukiyar jihar da sunan albashi, ya kara da cewa gwamnatinsa za ta dauki matasa aiki da zarar ta kammala aikin.

Gwamnan ya ce ya samu nasarar ganawa da masu sanya hannun jari na cikin gida da kasashen waje don nemo hanyoyin farfado da masana’antun jihar Bauchi.

Ya ce daga cikin ababen da suka faranta masa rai a shekarar 2020 har da fara aiki da shiri na musamman da a karkashin sa aka samar da daruruwan motocin safa da kafi-babur a farashi mai rahusa ga kungiyoyin direbobi da ‘yan Achaba

Daga karshe gwamnan ya yi kira ga al’umma da su fadaka da bayanan jami’an lafiya kan cutar Korona da ke barazana ga lafiyar al’ummar duniya.

Ya gudanar da addu’o’in na musamman ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya a shekarar 2020 da nema wa marasa lafiya sauki a wajen Allah.

SendShareTweetShare
Previous Post

Za Mu Haska Fim Din A Fadin Kasar Nan ‘The right choice’ Bayan Kammalawa – Kabiru Musa Jammaje

Next Post

Haduwar Jini (4)

RelatedPosts

Garban

Garban Kauye Farawa Ne Allurar Dinke Barakar Kumbotso – Muslihu Yusuf Ali

by Khalid Idris Doya
17 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana zaben Sabon shugaban Karamar...

Harkokin Noma

Sarkin Noma Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kokari Wajen Gyara Harkokin Noma

by Khalid Idris Doya
18 hours ago
0

Daga Bala Kukkuru, Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Umar...

Kwazon Tambuwal

Hobbasar Kwazon Tambuwal Na Fara Biyan Albashi Daga Haraji A 2023

by Khalid Idris Doya
2 days ago
0

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin...

Next Post
Haduwar Jini

Haduwar Jini (4)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version