Duk Da Matsalar Tsaro, Nijeriya Na A Hannu Na Gari – Lai Mohammed

Raba Kasa

Daga Mahdi M. Muhammad,

Ministan Yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, “duk da matsalolin tsaro da muke fuskanta a yanzu, Nijeriya na cikin amintattun hannaye’’.

Ministan ya bayar da tabbacin ne ranar Alhamis a Abuja lokacin da basaraken gargajiyar na Iyin-Ekiti, Oba Adeola Ajakaiye, Oluyin na Iyin-Ekiti suka kai masa ziyarar ban girma.

Ya kara da cewa, “bai kamata mu rinka yin wani abu da bai kamata ba ga kasar don hasashen ranar gobe kiyama. Yana da muhimmanci ga shugabanninmu a kowane mataki su bai wa mutane sakon bege a maimakon yin tsokaci da zai iya kara rura wutar rikici.”

Lai Mohammed ya yi kira musamman ga sarakunan gargajiya a kasar nan da su hada kai da gwamnatocin jihohinsu don tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

“Sarakunan gargajiya na da matukar muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin su. Wannan shine dalilin da ya sa ba za su iya ba kuma ba za a yi watsi da su ba, yayin da muke neman dawo da zaman lafiya da tsaro a duk fadin kasar,” in ji shi.

Ministan ya fada wa basaraken, wanda ya zo neman hadin gwiwa kan bunkasa yawon bude ido a yankinsa, cewa ba za a samu nasarar yawon shaklkatawa ba tare da tsaro ba.

Ya yi alkawarin sanya Kogon Esa da Okuta Abanijorin, wuraren shakatawa na bai daya na Iyin-Ekiti, a kan taswirar kasa da ta duniya don jan hankalin masu yawon bude ido.

A nasa bangaren, Oba Ajakaiye ya tabbatar wa da Ministan sha’awarsa da jajircewarsa don zaman lafiya a kasar.

Ya kuma jaddada cewa yin amfani da wuraren yawon bude ido a yankinsa zai bunkasa tattalin arzikin garin, jihar Ekiti da klkasa baki daya.

Exit mobile version